Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa arzikin Nijeriya ta’annati (EFCC) ta shigar da ƙarar tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja kan zargin halatta kuɗin haram da suka kai naira biliyan 84.
Hukumar ta gurfanar da tsohon gwamnan ne a ranar Alhamis tare da ƴan'uwansa uku Ali Bello da Dauda Sulaiman da kuma Abdulsalam Hudu.
EFCC tana tuhumarsa ne da laifuka da suka haɗa da halatta kuɗin haramun da rashin gaskiya da karkatar da kuɗaɗe fiye da biliyan 84, kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na X.
Ko da yake tsohon gwamnan da ɗaya daga cikin ƴan'uwansa Abdulsalam Hudu ba su halarci zaman kotun ba na ranar Alhamis, sai dai sauran mutanen da ake tuhumarsu tare Ali Bello da Dauda Suleiman sun halarci zaman kotun.
Mutanen sun “musanta duka zarge-zargen da ake yi musu” lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen.
A ƙarshen zaman, Mai Shari’a James Omotosho ya ɗage zaman kotun zuwa ranar 28 ga watan Maris ɗin shekarar 2024 don ci gaba da sauraren shari’ar.