Rundunar 'yan sandan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta tabbatar da kashe wasu mutane a wasu ƙauyuka biyu da ke karamar hukumar Kankara.
Wasu gungun 'yan bindiga ɗauke da manyan makamai ne suka kai farmaki ƙauyukan Gidan Boka da kuma Ɗan Nakwabo a kan babura a ranar Lahadi, inda suka kashe mutum 20 mazauna da 'yan sanda huɗu, da kuma wasu jami'an sa-kai biyu, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq ya shaida wa TRT Afrika Hausa.
''Da misalin karfe 3 na rana, an samu kiran gaggawa a hedkwatar 'yan sanda da ke garin Kankara, kan cewa wasu ‘yan bindiga ɗauke da manyan makamai a kan babura suna ta harbe-harbe, kana sun kai hari ƙauyuka biyu na karamar hukumar Kankara tare da kashe mutane da dama,'' a cewar Sadiq.
Ya kara cewa “‘yan bindigar sun yi wa jami’an tsaron da suka yi ƙoƙarin kai dauki kwanton ɓauna, inda aka yi ta musayar wuta tsakanin su, lamarin da ya bai wa 'yan bindigar damar halaka 'yan sanda hudu da kuma wasu jami'an sa-kai biyu."
Sai dai wani mazaunin ƙauyen Hassan Ya'u ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa, 'yan bindigar sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi, inda suka kashe mutum sama da 50, cikin su har da wani ɗan'uwansa, kana suka yi garkuwa da wasu mata da yara.
A halin da ake ciki dai rundunar 'yan sandan jihar ta Katsina ta ce tana aiki tuƙuru tare da masu ruwa da tsaki domin hana sake aukuwar lamarin da kuma ƙoƙarin kamo waɗanda suka aikata wannan mummunar aika-aika, in ji ASP Abubakar Sadiq.
Sannan ta ce tana gudanar da binkice tare da tura ƙarin ƙwararrun jami’anta da kayan aiki zuwa yankin da lamarin ya auku don ceto mutanen.
Matsalar tsaro a jihar ta Katsina na ci gaba da ta'azzara inda rahotanni suka ce an kai hare-hare da dama a kananan hukumomin Dutsin-Ma da Safana a cikin watan Yunin nan lamarin da yi sanadiyar kashe gomman fararen-hula.