MURIC ta ce "ma'aikatan sufurin jiragen sama da ke yajin aiki a Nijeriya sun juya da jirgin da aka tura don kwaso maniyyata daga Nijeriya zuwa Saudiyya./Hoto:  National Hajj Commission of Nigeria

'Yan ƙungiyar ƙwadago da ke yajin aiki a Nijeriya sun hana wani jirgi ɗaukar maniyyata aikin Hajji daga ƙasar zuwa Saudiyya ranar Litinin, a cewar ƙungiyar da ke rajin kare haƙƙoƙin Musulmai ta Muslim Rights Concern (MURIC).

Wata sanarwa da shugaban MURIC Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar ranar Litinin da yamma ta bayyana fargaba game da tasirin da yajin aikin ƙungiyar ƙwadago ta NLC zai yi kan "rayuwar dubban mahajjatan Nijeriya da kuma aikin kwashe su da hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON) take yi."

MURIC ta ce "ma'aikatan sufurin jiragen sama da ke yajin aiki a Nijeriya sun juya da jirgin da aka tura don kwaso maniyyata daga Nijeriya zuwa Saudiyya. An tilasta wa jirgin komawa filin jirgin saman Jedda ba tare da kowa a cikinsa ba."

"A gefe guda, yanzu dubban maniyyata na cikin hatsari saboda an dakatar da jigila ta zuwa aikin Hajji. Dubban maniyyata sun rasa yadda za su yi bayan da suka bar gidajensu zuwa filiyen jiragen sama," in ji MURIC.

Ƙungiyar MURIC ta ce ba ta ga dalilin da zai sa NLC ta soma yajin aiki a yayin da ake ƙoƙarin kwashe maniyyata fiye da 60,000 daga Nijeriya domin kai su Saudiyya su sauke farali ba.

Ta yi kira na NLC ta janye yajin aiki tare da yin sulhu da gwamnati domin samun matsaya.

Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na Nijeriya ta tsunduma yajin aiki a faɗin ƙasar ranar Litinin ne bayan sun kasa samun matsaya da gwamnatin tarayya kan mafi ƙarancin albashi da kuma buƙatarsu ta neman a janye ƙarin da aka yi na kuɗin lantarki a faɗin ƙasar.

Shugabannin ƙwadagon sun ce ba za su ci gaba da amincewa da N30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Nijeriya, musamman ganin cewa ko a hakan ma akasarin gwamnonin jihohi ba sa iya biyan ma'aikata, shekara biyar bayan tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya sanya wa dokar sabunta albashi hannu.

A taron ƙarshe da ƙungiyoyin ƙwadagon suka yi da gwamnati kafin ayyana tafiya yajin aikin, sun yi fatali da aniyar gwamnati ta biya N60,000 a matsayin mafi ƙaranci albashi a Nijeriya. Duka ƙungiyoyin NLC da TUC sun dage cewa dole ne gwamnati ta riƙa biyan aƙalla N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

TRT Afrika