Tun bayan da ya mika wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ragamar mulkin Nijeriya a Dandalin Eagle Square a Abuja ranar 29 ga watan Mayu, Muhammadu Buhari ya wuce Daura don ci gaba da rayuwarsa, kamar yadda ya sha fada cewa zai yi hakan.
Sai dai a cikin kwana fiye da 100 da ya yi da barin mulki, an yi ta jiyo duriyarsa ta hanyar wallafa hotunan ziyarar da mutane ke kai masa a shafukan sada zumunta da ma ta bakin mataimakansa kan watsa labarai.
A wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Alhamis, ya fayyace irin yadda rayuwa ta kasance wa Muhammadu Buhari a tsawon wannan lokaci a mahaifarsa ta Daura.
Buhari ya shafe shekara takwas a matsayin shugaban kasar Nijeriya a wa’adi biyu, inda a lokacin saukarsa ya dinga shan yabo da suka daga wajen ‘yan kasar.
Ga dai jerin abubuwan da Garba Shehu ya ce sun wakana a kwana 100:
1. Ya zabi zama a Daura ne saboda ya yi nisa da Abuja don kar ya rika raba hankalin sabuwar gwamnatin APC da kuma fatan cewa nisan da ya yi zai sa ya samu isasshen hutu da kula da gonarsa, wacce ba ta samun kulawa sosai a lokacin da yake Abuja.
2. Yana zuwa gonarsa sau hudu a sati kuma yana farin cikin yadda a yanzu amfanin gonarsa da dabbobinsa ke bunkasa. Yana samun hutu sosai kuma hakan ba ya shafar kula da gonar.
3. Don ganin ya dore da zuwa gona sau hudu a satin, yana da tsari na yadda al'amuransa za su kasance duk mako, wanda aka shirya masa tun a lokacin da yake fadar shugaban kasa.
4. An tsara masa yadda zai rika karbar baki masu ziyara, amma akwai mutane da dama wadanda kawai sai su buga babur ko motarsu su tafi wajensa a Daura don a tunaninsu koyaushe lokacin karbar baki ne a gare shi.
5. Daga cikin “baki na musamman” da yake yawan samu har da ‘ya’yan jam’iyya da kungiyoyin al’ummomin kauyuka da shugabannin al’ummomi da ma sauran kwararru a fannoni daban-daban. Da ma wadanda suka ci moriyar gwamnatinsa sosai.
6. Ya rika fatan cewa matakin cire tallafin mai da gwamnatin Tinubu ta yi zai rage rububin masu hawa motocinsu takanas zuwa ganinsa a Daura daga sassan kasar da dama don ganinsa.
7. Amma sai ya fahimci cewa maimakon su ci gaba da zuwa daya bayan daya, abokansa, ciki har da marasa galihun a yanzu sai su yi kungiya su yi hayar motocin bas-bas su hada kudi su biya su je su gan shi su yi hira da shi.
Malam Garba ya ce a yayin da wasu a kasar suke farin cikin cewa ya bar mulki, akwai wasu da dama da ke ci gaba da nuna masa soyayya da kauna.
Baya ga bayanan yadda rayuwar tsohon shugaban kasar ke kasancewa a Daura, Malam Garba ya kuma tuno da wasu nasarorin da Buhari ya cimma a shekara takwas da ya yi yana mulki.
“A cikin shekara takwas da ya mulki Nijeriya, Muhammadu Buhari ya dauki matakai da dama, kuma a matsayinsa na da’adam, ba za a rasa waje daya ko biyu da ya yi kuskure ba.
“Amma kuma, babu wanda zai iya yin tababa a kan aniyarsa a lokacin daukar wadannan matakan, ko da kuwa masu suka ne.
“Babu wani bangare da gwamnatin Buhari ba ta tabo ba ta hanyar samar da gagrumin sauyi a shekara takwas din da ya yi, ya kara da cewa.