Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka ta gabatar da kungiyar kwallon kafa ta Yanga da ke Tanzania domin takarar lashe kulob din maza na shekara. Hoto/ Yanga CS/X        

Daga Nuri Aden

Tanzania, kasar da ke da Tsaunin Kilimanjaro da Serengeti da kuma Tsibirin Zanzibar. Ta ina “Kyakkyawan wasa” wanda yake da biliyoyin mabiya ke da alaka da daya daga cikin kasashe mafi kyau a Afirka?

Ko kuma a rayuwar Mbwana Samatta da Novatus Miroshi? Maraba da zuwa sabuwar Tanzania. Zuwa Dar es Salam, da kuma fitaccen filin wasa na Mkapa. Rana ce ta 20 ga watan Oktoban 2023.

Filin wasan yana dauke da magoya baya 60,000 wadanda za su kalli yadda za a rubuta tarihi a daidai lokacin da kungiyar Simba ta kasar za ta kara da kungiyar Al Ahly ta Masar a wurin bude gasar African Football League.

Kulob din Tanzania na Simba na daga cikin wadanda suka kara a gasar Africa Football League. Hoto/CAF

Filin wasan da kasar baki daya da suke kallo ta talabijin sun ta jin ba dadi a yayin da wani kulob na nahiyar ke kan gaba a wasan tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Sai dai Kibu Denis na kungiyar Simba ya zura kwallo a raga inda kowa ya yi ta jin dadi.

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan da kuma shugaban FIFA Gianni Infantino da kuma tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger wanda a yanzu shi ne shugaban cibiyar ci-gaban kwallon kafa inda duka suka tashi suna tafi.

A sabuwar gasa

Ga masu sa ido, an kimanta Tanzania ta 31 a cikin kasashe 56 na Afirka, a duniya kuma ta 121.

Simba ta zama ta 13 a cikin kungiyoyin kwallon kafa ta Afirka. Hoto/Simba

Sai dai ga wannan kasa da ke Gabashin Afirka, ya zama abin jinjina a daidai lokacin da darajar kwallon kafarta ta kara daukaka ko da yake makwaftanta sun sauka daga mataki na 10 zuwa na 20 a lokacin. Kuma wannan na fitowa ne daga kasa da ke ta 156 a 2016.

Duk da cewa Uganda a yanzu tana ta 90 Kenya kuma 110, Tanzania a halin yanzu za ta wakilci yankin a gasar AFCON ta 2023 wadda ake sa ran za a gudanar a Janairun 2024 a Cote d'Ivoire.

Ana sa ran wannan wasan zai samu karbuwa inda kasar ke shirin karbar bakuncin gasar, tare da Kenya da Uganda, bayan shekaru hudu.

Kungiyar mata na samun daukaka

Kungiyar kwallon kafa ta JKT Queens ta Tanzania za ta kara a gasar kwallon kafa ta mata a Afirka. Hoto/CAF

Duk da cewa kungiyar kwallon kafa ta Tanzania ta mata ta samu nasara a gasar mata ta Cosafa a 2021, ainihin nasarar ta zo ne bayan shekara guda lokacin da 'yan matan suka cancanci shiga gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekara 17.

Wannan ne karo na farko da kungiyar kwallon kafa ta Tanzania ta maza ko mata da ta taba kaiwa wannan matakin. A lokacin gasar, kungiyar matan ta Serengeti ta samu nasara kan matan Faransa da ci 2-1 da kuma yin kunnen doki da matan na Canada da ci 1-1 domin samun gurbi a zagayen daf da na kusa da na karshe.

Gasa tsakanin kungiyoyin cikin gida

A kakar da ta gabata, kungiyar kwallon kafa ta Yanga FC da ke Tanzania da kuma abokiyar adawarta Simba sun kai zagayen karshe na gasar Confederations ta CAF.

Simba wadda a halin yanzu ta kai mataki na 13 a nahiyar Afirka, ta kasance kungiya daya tilo daga Tanzania wadda ta wakilci kasar a gasar African Champions League har ta kai zagayen daf da kusa da na karshe. Simba da Yanga wadanda duka kungiyoyi ne na Tanzania su kadai ne suka shiga gasar CAF ta kakar bana daga Gabashin Afirka.

Dabin da ake yi tsakanin Yanga da Simba ya jawo karin ce-ce-ku-ce a shafin sada zumunta inda duka kungiyoyin ke neman rinjaye.

Simba na da sama da mabiya miliyan hudu a Facebook sai kuma Yanga na da rabin hakan.

A shafin X, mutum miliyan 1.4 suna bibiyar Simba sai kuma Yanga na da mabiya 281,000. Sai kuma a shafin Instagram Simba na da miliyan 5.5 sai kuma abokan hamayyarsu na da miliyan 2.8. Irin wannan gwagwarmayar da ake yi ta neman mabiya na kara jawo masu son zuba jari a cikin

Samun kudin shiga

Babban mai daukar nauyin gasar kwallon kafar Tanzania wato bankin NBC ba da dadewa ya saka hannu kan yarjejeniyar shilling biliyan 32.6 na Tanzania.

A 2021, gasar ta saka hannu kan damar nuna wasan a talabijin kan kudi TZS biliyan 225.6.

Ganin cewa kwallon kafa na daga cikin abubuwan da ke ja a kasar, masu kungiyoyin kwallon kafa na zuba biliyoyin kudi domin kawo sauyi ga yanayin wasan.

Mai kungiyar kwallon kafa ta Simba Mo Dewji ya zuba TZS biliyan shida, Gharib Said Mohamed mai Yanga shi ma ya bi layi. Sakamakon hakan, darajar gasar kwallon kafar kasar ta karu zuwa TZS biliyan 300.

Shugaba Hassan ta kasance daya daga cikin masu ruwa da tsaki wurin habakar wasan - inda take bayar da lada ga kungiyoyin da ke samun nasara inda har a wani lokaci take kawo misali da kwallon kafa a lokacin muhawara a gaban majalisa.

Sautin kida

A Tanzania, kwallon kafa na tafiya ne tare da bangaren wakoki. Irin su Ali Kiba da kuma Diamond Platnumz na halartar wuraren kwallo inda har suke yi wa kungiyoyin wakoki.

An ta yin wakoki ga Mbwana Samatta, wanda ya kasance zakaran kwallon kafar shekarar 2016, haka kuma dan Tanzania na farko da ya soma wasa a gasar Firimiya ta Ingila.

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na kasar da kuma mai horar da 'yan wasansu na kasa a yanzu ya koma kungiyar POAK FC ta Girka sakamakon zama a Aston Villa, Fenerbahce, Antwerp da Genk.

Dan wasan kasar Novatus Miroshi, mai shekara 21, dan wasan Shakhtar Donetsk ne kuma matashin dan kasar Tanzania da ya taba taka leda a gasar Zakarun Turai.

 Mawakin Tanzania Ali Kiba a lokacin wasan kwallo mafi girma a Tanzania. Hoto/Ali Kiba 

Kwallon kafa a nan ta dauki harami. Kuma kamar Simba, Pumbaa da Timon, yanzu magoya baya na iya yin kururuwa, "Hakuna Matata!"

TRT Afrika