Jam'ian tsaron Nijeriya na ikirarin samun nasara a farmakin da suke kai wa maboyar 'yan bindiga. Photo/Nigerian Army

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama, akasarinsu mata da yara a Jihar Zamfara da ke arewacin Nijeriya.

‘Yan bindigan sun kai harin ne a ranar Juma’a a kauyen Wanzamai da ke Karamar Hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara, kamar yadda wasu mutum uku da ke yankin suka tabbatar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Zamfara Mohammed Shehu ya tabatar da faruwar wannan lamarin sai dai ya ce adadin da ake zuzutawa na jama’ar da aka sace bai kai 80 ba kamar yadda wasu kafafe suka ruwaito.

Ya bayyana cewa rahoton da 'yan sanda suka samu na cewa mutum tara ne da suka hada da yara da mata aka sace.

Sai dai Musa Usman, wanda aka sace dansa mai shekara 14 mai suna Ibrahim ya bayyana cewa yara da matan kauyen na tsaka da sharar gona da kuma tsintsar itacen wuta sai maharan suka far musu tare da tasa keyarsu zuwa cikin daji.

“Yara daga gidaje daban-daban sun je tsintar itacen wuta, wasu kadan kuma suna hanyar gona domin neman aiki inda a lokacin ne aka sace su,” kamar yadda Usman ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta waya.

Haruna Noma wanda shi ma daya daga cikin iyayen yaran da aka sace ne ya ce wadanda aka sacen sun fito daga kauyuka biyu da ke makwaftaka da Wanzamai wato Kucheri da Danwuri inda aka sace lokacin da suka je Wanzamai gyaran gona.

Mazaunan kauyen sun ce har yanzu ‘yan bindigan ba su yi magana kan kudin diyyar da za a biya su ba.

Amina Tsafe wadda ita ma aka sace ‘yarta ta ce akasarin yaran da aka sace na tsakanin shekara 12 zuwa 17.

Masu garkuwa da mutane a Najeriya akasari na ajiye wadanda suka sace tsawon watanni idan ba a biya kudin da za a fanshe su ba, haka kuma suna bukatar jama’ar kauye su biya kudi domin barin su domin su yi noma.

Sace jama’a a Zamfara na zuwa ne kwanaki bayan an sace akalla dalibai takwas a Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.

Hukumomi a Kadunan sun ce suna daukar matakai domin ceto daliban da aka sace a ranar Litinin.

Rundunar sojin Nijeriya na ta kai farmaki dazukan da ‘yan bindiga ke boyewa. Lamarin garkuwa da mutane ya ragu cikin ‘yan watannin da suka gabata bayan farmakin da aka kai.

Amma lamarun baya-bayan nan da suka faru kan iya sa jama’a saka ayar tambaya kan batun tsaro kasar.

TRT Afrika da abokan hulda