Wannan ce Umrah ta karshe da Shugaba Buhari yake yi a matsayin Shugaban Nijeriya / Hoto: Haramain Sharifain

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce babban aiki mafi muhimmanci da ke gaban Musulman duniya a yau shi ne yada akidu da ilimin addinin Musulunci na gaskiya.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a ranar Laraba a birnin Madina na kasar Saudiyya, a ziyarar aikin Umara da yake yi.

A cikin wata sanarwa da aka fitar mai dauke da sa hannun Malam Garba Shehu, mai bai wa shugaban shawara kan kafafen yada labarai, Buhari ya kuma yaba wa gwamnatin Saudiyyar bisa yadda ta samar da kayayyakin zamani wajen yada Musulunci da sanin manufarsa a ilimance kuma ta hanya mafi inganci.

Ya yi wannan bayani ne yayin wani rangadi a wajen baje-kolin kasa da kasa da kuma zagaya gidan adana kayan tarihin Annabi Muhammad SAW da Sakafar Musulunci a wani bangare na ayyukan da yake yi a Saudiyya.

Shugaban Nijeriyar ya ce al'ummar Musulmai na bukatar tsari ingantacce da zai bayar da hikima da ilimi don kyakkyawar fahimtar addinin.

Ya ce ”Ya zama dole a samu kyakkyawar fahimtar addinin domin a magance munanan akidu da fahimta da ake danganta masa, don a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a duniya.”

Ya yaba wa mahukuntan Saudiyya bisa yadda suka yi kokarin yada sakafar Musulunci a duniya, amma kuma ana bukatar karin ayyuka da dama.

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa gidan adana kayan tarihin “Na adanawa tare da gabatar da Musulunci tsantsa yadda yake.

"Yana yin hakan ta hanya mafi daraja da aka koyar da shi da ke cewa shi sako ne na rahama da kauna da adalci da zaman lafiya da matsakaicin ra’ayi, kuma ana bayyana hakan ta hanyar hotuna da kyawawan gine-gine da ma’anoni.”

Buhari ya kuma kara da cewar “Wannan gidan adana kayan tarihi na kuma bayar da cikakken tarihin rayuwar Annabi SAW da kyawawan halayensa da dabi’unsa masu kyau da koyarwarsa, ta hanyar binciken kimiyya da amfani da kayan fasahar sadarwa na zamani.”

TRT Afrika da abokan hulda