Kamfanin mai na Nijeriya, NNPCL, ya musanta zargin da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar ya yi cewa Shugaba Bola Tinubu yana ƙoƙarin sanya harkokin kasuwancinsa cikin na gwamnati da zummar mallake dukiyar Nijeriya.
A wata sanarwa da kakakin NNPCL, Olufemi Soneye, ya fitar ranar Alhamis ya musanta zargin da Atiku ya yi cewa an tsawaita wa'adin Mele Kyari a matsayin shugaban NNPC Ltd ne don saka masa saboda NNPCL ya sayi kamfanin mai na OVH wanda ya yi iƙirarin cewa Mr. Wale Tinubu ne yake da kashi 49 na hannayen jarinsa.
Olufemi Soneye ya ce Shugaba Tinubu da Wale Tinubu babu ɗaya daga cikinsu da ke da hannu a sayen kamfanin na OVH.
''A lokacin da NNPCL ya sayi OVH a 2022, kamfamin Oando (wanda Wale Tinubu ke da hannayen jari a cikinsa), ya riga ya cire hannayen jarinsa daga kamfanin OVH, inda ya bar shi a hannun kamfanin - Vitol da kuma Helios'', in ji sanarwar.
''A shekarar 2016 kamfanin Oando ya fara janye hannayen jarinsa, inda kamfanonin Vitol da Helios suka zama mamallakan kamfanin kacokan, abin da ya sa aka sauya masa suna daga Oando zuwa OVH," a cewar NNPCL.
Ta ƙara da cewa, "A 2019 Oando ya kammala cire hannayen jarinsa daga kamfanin OVH, abin da ya sa kamfanonin Vitol da Helios suka mallaki kashi Hamsin-Hamsin na hannayen jarin kamfanin."
Sanarwar ta ce bayan NNPCL ya kammala sayen OVH sai duka gidajen man NNPCL da na OVH suka zama rassan kamfanin NNPCL.
"Amma bayan samun shawarwari daga ƙwararru da kuma yin la'akari da ƙa'idojin kasuwanci, NNPCL ya haɗe duka gidajen man kamfanonin biyu, daga bisani ake kiransu da sunan NNPCL, a cewar NNPCL.