Kasashen da ke makwaftaka da Sudan sun karbi bakuncin 'yan gudun hijira kusan 50,000 tun bayan da aka soma wannan rikicin. Photo/Reuters

Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta dakatar da akasarin ayyukanta a Khartoum babban birnin Sudan da wasu sassa na kasar sakamakon karuwar matsalolin tsaro.

A wata sanarwa da hukumar ta UNHCR ta fitar, ta ce Khartoum da kuma yankunan Darfur da Arewacin Kordofan sun zama yankunan da ke da matukar hatsari a gareta ta gudanar da ayyukanta duk da cewa ana bukatar agajin ceto rayuka.

Hukumar ta ce mutum 50,000 zuwa yanzu sun tsere daga Sudan tun bayan da aka soma rikici a kasar makonni biyu da suka wuce tsakanin rundunar sojin kasar da kuma rundunar RSF.

An ci gaba da jin karar fashewa da harbe-harben bindiga a ranar Asabar a fadin Khartoum duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’o’i 72 da bangarorin da ke rikici suka amince da ita.

Kasashen da ke makwaftaka da Sudan da suka hada da Chadi da Kudancin Sudan da Masar da Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka na ci gaba da karbar ‘yan gudun hijira, kamar yadda hukumar UNHCR ta sanar.

“A Masar, gwamnatin ta bayar da rahoton mutum 16,000 sun tsallaka zuwa kasar, 14,000 ‘yan Sudan ne,” in ji hukumar.

A Chadi, ‘yan gudun hijira 7,500 cikin akalla 20,000 wadanda suka tsallaka iyaka a makon da ya gabata su ma an tantance su.

Kusan mutum14,000 wadanda akasarinsu ‘yan Sudan ta Kudu ne sun gudu zuwa kasar.

A Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika da Habasha, ba a tantance hakikanin adadin jama’ar da suka yi gudun hijira ba zuwa kasashen, sai dai hukumar ta ce ba a samu adadi mai dumbin yawa ba.

Amma duk da haka, akwai motsin jama’a a sansanin ‘yan gudun hijiran da ke cikin Sudan.

“Mun samu rahoto kan cewa kusan ‘yan gudun hijira 33,000 sun gudu daga Khartoum domin neman mafaka a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Jihar White Nile, akwai 2,000 da je Gedaref sai 5,000 zuwa Kassala tun bayan da rikicin ya barke, inda suke son tsira da rayuwarsu,” in ji hukumar.

TRT Afrika da abokan hulda