Duk kokarin da gwamnati ta yi na shawo kan NLC kada ta yi yajin aikin na gargadi abin ya ci tura. Hoto/Getty Images

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya NLC ta soma zanga-zanga a ranar Litinin a faɗin ƙasar inda take adawa da ƙarin kuɗin wutar lantarki da gwamnatin Nijeriya ta yi da kuma janye tallafin man fetur.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin Nijeriya ta sanar da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga kwastamomi waɗanda ke rukunin A, inda za su rinƙa biyan naira 225 a duk kilowatt ɗaya a maimakon naira 68 da suke biya a baya.

Rahotanni sun ce tun da sanyin safiya 'yan ƙwadagon suka yi wa hedikwatar kamfanin rarraba wutar lantarki ta Jos da ke Jihar Filato ƙawanya inda suka hana ma'aikatan kamfanin shiga cikin ofis.

Haka kuma rahotannin sun ce ‘yan ƙwadagon sun yi ƙawanya a ofishin hukumar da ke sa ido kan kamfanonin lantarki NERC wanda hakan ya ja ma’aikatan hukumar suka kasa shiga ofishin.

A Abuja babban birnin Nijeriya, 'yan kwadagon sun je gaban ofishin na NERC inda suke buƙatar gwamnatin ƙasar ta janye matakin da ta ɗauka na ƙara farashin lantarkin.

Tun da farko ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun bayar da wa’adin zuwa 12 ga watan Mayu kan hukumomin na Nijeriya su janye wannan ƙarin da suka yi.

Tun bayan ƙarin kuɗin wutar, ƴan Nijeriya da dama sun ta bayyana rashin jin daɗinsu dangane da lamarin inda suke cewa hakan zai ƙara musu tsadar rayuwa sakamakon ƙarin na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan ƙasar ke fama da raɗaɗin janye tallafin man fetur.

TRT Afrika