Ko a ranar Juma’ar da ta gabata sai da Lakurawan suka kashe aƙalla mutum 15 a kusa da garin Mera a Ƙaramar Hukumar Augie da ke Jihar Kebbi. / Hoto: DHQ

Ƙungiyar Dattawan Arewa ta ACF ta buƙaci sojojin Nijeriya su yi ƙoƙari domin murƙushe sabuwar ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa wadda ta ɓulla a Sokoto da Kebbi da ke arewacin Nijeriya.

Ƙungiyar ta ACF bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ɗauke da ta sa hannUn sakataren watsa labaranta Farfesa Tukur Muhammad Baba.

Ƙungiyar ta buƙaci sojojin ƙasar su yi amfani da duk wasu kayan aikinsu domin tabbatar da cewa sun murƙushe ‘yan ta’addan.

ACF ɗin ta yi gargaɗi kan cewa kada a ɗauki wannan sabuwar ƙungiyar da wasa ko kuma a bar ta cikin al’umma kamar yadda aka yi sakaci da batun Boko Haram da rikicin manoma da makiyaya da ‘yan garkuwa da mutane.

Ƙungiyar ta ACF ta ce ɓullar wannan sabuwar ƙungiyar ta Lakurawa ta jawo buƙatar kafa wata sabuwar rundunar ƙawance ta ƙasa da ƙasa tsakanin Nijeriya da makwabta inda ta ce akwai buƙatar a shawo kan Jamhuriyar Nijar domin ta sa kanta a ciki.

“Akwai buƙatar a yi amfani da ziyarar da babban hafsan hafsan hafsoshin Nijeriya, Janar Christopher Musa ya kai Jamhuriyar Nijar a farkon wannan shekarar a matsayin wata dama don ƙoƙarin da ake yi na ƙasa da ƙasa domin murƙushe ta’addanci,” in ji sanarwar.

A makon da ya gabata ne dai Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da ɓullar ƙungiyar Lakurawa a yankin Sokoto da Kebbi.

Ko a ranar Juma’ar da ta gabata sai da Lakurawan suka kashe aƙalla mutum 15 a kusa da garin Mera a Ƙaramar Hukumar Augie da ke Jihar Kebbi.

TRT Afrika