Ministar Harkokin Wajen Ghana Shirley Ayorkor Botchwey. / Hoto: AFP

Mambobin ƙungiyar ƙasashen renon Ingila sun zaɓi Shirley Ayorkor Botchwey a matsayin sakatare janar ta ƙungiyar ƙasashen mai mambobi 56 wadda ke ƙarƙashin jagorancin Sarkin Ingila, kamar yadda ƙungiyar ta Commonwealth ta sanar a ranar Asabar.

Ta sanar da hakan ne a rana ta ƙarshe ta taron wanda ake gudanarwa a Samoa wanda ya samu halartar Sarki Charles da kuma Camilla.

Wakilai daga ƙasashe waɗanda akasarinsu Birtaniya ce ta yi musu mulkin mallaka sun halarci taron wanda aka soma a ƙasar da ke tsibirin tekun Pacific a ranar Litinin, inda daga cikin manyan abubuwan da aka tattauna suka haɗa da batun cinikin bayi da kuma barazanar sauyin yanayi.

"Yau a # CHOGM2024, shugabannin Commonwealth sun zabi Hon Shirley Ayorkor Botchwey, a halin yanzu ministar harkokin wajen Ghana, a matsayin sakatare-janar ta Commonwealth," in ji Commonwealth a shafinta na X.

Shirley Ayorkor Botchwey ta kasance ɗaya daga cikin masu goyon bayan biyan diyya dangane da cinikin bayi da mulkin mallaka da aka yi wa ƙasashe kuma a halin yanzu ta karɓi wannan muƙamin ne daga Patricia Scotland wadda take kan muƙamin tun daga shekarar 2016.

Tarihi mai raɗaɗi

Da safiyar Asabar, Sarkin Ingila tare da mai ɗakinsa sun bar Samoa bayan halartar taron inda sarkin ya tuna da tarihi mai "raɗaɗi" na ƙasashen da aka yi wa mulkin mallaka, a daidai lokacin da ake ta matsin lamba ga ƙasashen da suka gudanar da mulkin mallaka su biya diyya dangane da abubuwan da suka aikata.

Charles a ranar Juma'a ya ce a cikin jawabin da ya yi a taron cewa ya fahimci "daga sauraron mutane a fadin Commonwealth yadda abubuwan da suka fi muni a baya suke ci gaba da tada hankali".

"Yana da muhimmanci, saboda haka, mu fahimci tarihinmu, tare da ɗora mu a kan hanya domin yin abubuwan da suka dace a nan gaba," in ji shi.

Reuters