An kulle Ministan Kudi da Tsare-Tsare  Amos  Lugoloobi har sai ranar 20 ga watan Afrilu inda za a cigaba da shari'a. Hoto/Uganda anti-corruption Unit  @AntiGraft_SH

Masu gabatar da kara a Uganda sun sake tuhumar ministan gwamnati da zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka jibanci sama da fadi da kwanukan rufi da aka tanada saboda marasa galihu.

An gurfanar da ministan kudi da tsare-tsare Amos Lugoloobi a gaban kotu a Kampala babban birnin Uganda, amma ya musanta zarge-zargen da ake yi masa.

A kalla akwai manyan jami’an gwamnati 22 da suka hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Shugaban Majalisar Dokoki da Ministoci da ake zargi na da hannu a wannan badakala.

Shugaban Kasar Uganda Yoweri Museveni da ake zargin gwamnatinsa da rashin niyyar magance cin hanci da rashawa, ya bai wa masu bincike umarnin bincika da kama masu hannu a wannan badakala sannan a hukunta su daidai da yadda doka ta tanada.

A watan Fabrairu ne aka samu labarin badakalar bayan da Jaridar New Vision ta ruwaito cewa jami’ai sun kama ‘yan uwan Minista Mary Kitutu a cikin wata mota suna sayar da kwanukan rufi da aka saya don amfanin masu karamin karfi a kasar.

Labaran da jaridar ta New Vision ta fitar sun bayyana cewa akwai dubban kwanukan rufi da jami’an gwamnatin suka raba a tsakaninsu.

Game da Lugoloobi, jaridar ta buga hoton wani wajen kiwon awaki da aka rufe da kwanon gwamnati da aka tanada saboda talakawa masu karamin karfi.

Akwai cin hanci da rashawa sosai a ayyukan gwamnati a Uganda, amma da wahala a samu wani jami’i da aka hukunta.

AP