Tuwona maina: ‘Yan majalisar dokokin Kenya za su auri juna

Tuwona maina: ‘Yan majalisar dokokin Kenya za su auri juna

‘Yan majalisar sun hadu da juna a lokacin yakin neman zaben da aka gudanar a bara.
'Yan majalisar sun hadu ne a wurin yakin neman zabe

Wasu mambobin majalisar dokokin Kenya biyu sun shirya kafa tarihi inda za su zama ‘yan majalisa na farko da suka auri juna.

Amarya, mai suna Murang’a da ke wakiltar Betty Maina, ta amince da bukatar neman auren ta da dan majalisa Mathira MP Eric wa Mumbi ya mika yi a karshen makon jiya, ta kuma yada hotuna a shafukan sada zumunta.

Ta rubuta “Masoyina Eric, ka hadu fa”. A baya dukkan su sun taba yin aure. Dukkan su ‘yan majalisa ne karkashin gwamnatin hadaka mai ci.

Mataimakin Shugaban Kasar Kenya Rugatha Gachagua ne zai jagoranci dangin ango a ranar Asabar mai zuwa don kai sadaki gidan surukansu.

Bisa al’adarsu ana bayar da kudi da kyaututtuka don yaba wa iyayen amarya.

Angon ya shaida wa kafafen watsa labarai cewa ya hadu da amaryar tasa a 2022, ya kuma gano tana da duk wani abu da yake son gani tare da matar da zai aura.

TRT Afrika da abokan hulda