Mahukunta a Ankara sun jaddada goyon bayansu ga kasancewar Sudan a matsayin dunƙulalliyar ƙasa mai cin gashin kanta. / Hoto: AP

Turkiyya ta yi matuƙar nuna damuwarta game da yadda yaƙi yake ta'azzara a Sudan, musamman musgunawar da ake yi wa fararen-hula a jihar Al Jazirah.

"Mun yi matuƙar damuwa game da mayuacin hali na rashin jinƙai da ake ciki a Sudan da kuma hare-hare da ake kai wa fararen-hula a jihar Al Jazirah lamarin da ya keta dokokin bayar da jinƙai," a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ranar Lahadi.

Ma'aikatar ta jaddada kiran da ta yi na buƙatar tsagaita wuta "ba tare da ƙarin ɓata lokaci ba da kuma maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali."

Ta ƙara da cewa akwai buƙatar ɗaukar matakai cikin hanzari "domin mayar da mutane gidajensu da bayar da agajin jinƙai a gare su a-kai-a-kai."

Sanarwar ta jaddada ƙudurin Turkiyya na tabbatar da 'yancin Sudan a matsayin "dunƙulalliyar ƙasa mai cin gashin kanta da haɗin-kai."

A matakin ƙasar na nuna goyon baya ga Sudan, mahukunta a Ankara sun yi alƙawarin ci gaba da kai kayan agaji da zummar "kawar da mawuyancin halin da al'ummar Sudan suke ciki," in ji sanarwar.

Dagulewar yaƙi a jihar Al Jazirah

Jihar Al Jazirah ta ƙasar Sudan ta kasance wani filin-daga bayan wani kwamandan dakarun rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces (RSF) Abu Aqla Kaykal ya sauya sheƙa zuwa ɓangaren gwamnati.

A wani abu da ake kallo a matsayin gagarumin koma-baya ga rundunar RSF, kwamandan ya koma ɓangaren rundunar sojin Sudan tare da abin da rundunar sojin ta bayyana da "manyan dakarunsa" .

Babbar jami'ar hukumar bayar da agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan, Clementine Nkweta-Salami, ta ce dakarun RSF sun ƙaddamar da manyan hare-hare a gabashin jihar Al Jazirah daga 20 zuwa 25 ga watan Oktoba.

TRT World