Wai jirgin ruwan Turkiyya ɗauke da kayan agaji masu nauyin fiye da tan 2,400 ya tashi daga tashar jiragen ruwa ta Mersin ranar Asabar inda ya nufi Sudan domin taimaka wa mutanen da yaƙi ya ɗaiɗaita.
An aika kayan agajin ne ƙarkashin Hukumar Kai Ɗauki kan Bala'o'i da Bayar Da Agajin Gaggawa ta Turkiyya (AFAD), tare da tallafin Ma'aikatar Kiwon Lafiya, Ƙungiyar Bayar da Agaji ta Turkish Red Crescent, da ƙungiyoyi da dama masu zaman kansu.
Kayan agajin sun haɗa da abinci, magunguna, tufafi, makwancin wucin-gadi, a cewar Okay Memis, shugaban AFAD.
Ana sa rai jirgin ruwan, mai suna Sardes, zai isa Sudan a makon gobe, a cewar Oktay.
Al'ummar Sudan na ci gaba da fama da bala'in yunwa sakamakon yaƙin da aka kwashe watanni 15 ana yi tsakanin sojojin Sudan da rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces (RSF).
Yaƙi ya raba miliyoyin mutane da muhallansu
An ƙiyasta cewa kusan mutum 16,000 suka mutu sakamakon yaƙin. Kazalika harkokin kiwon lafiya na ƙasar sun durƙushe.
Hukumar Lura da Masu Ƙaura ta Duniya (IOM) ta ce yaƙin wanda aka soma a watan Afrilun 2023 ya raba mutum miliyan 7.7 da muhallansu sannan fiye da mutum miliyan 2 sun fice daga ƙasar zuwa maƙota don yin gudun hijira, kuma kashi 55 daga cikinsu yara ne.
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya ce Sudan ce ƙasar da yaranta suka yin gudun hijira, inda aka ƙiyasta ce yara sama da miliyan 5 ne suka zama 'yan hijira.
IOM ta ce kashi 36 na mutanen da yaƙin ya raba da muhallansu mazauna yankin babban birnin ƙasar Khartoum ne, kashi 20 daga Kudancin Darfur, sannan kashi 14 daga Arewacin Darfur.