Da yake magana a wajen wani taron manema labarai a Ankara, Shugaban Turkiyya Erdogan ya gode wa shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud da Firaminitsan Ethiopia Abiy Ahmed saboda “sasantawa mai tarihi” da suka yi. / Hoto:AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jinjina wa shugaban Somaliya da firaministan Habasha saboda cim ma "sasantawa mai cike da tarihi tare da gagarumar sadaukarwa" a yayin tattaunawar zaman lafiya da Ankara ta jagoranta, wacce ake sa ran za ta kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu game da ballewar yankin Somaliland.

Da yake magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa a Ankara da yammacin Alhamis, Erdogan ya gode wa Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud da Firaministan Habasha Abiy Ahmed tare da bayyana cewa bangarorin biyu sun amince da sanarwar hadin gwiwa don warware takaddamar dake tsakaninsu.

Erdogan ya ce, "Mun dauki matakin farko zuwa wani sabon shafi kan zaman lafiya da hadin gwiwa tsakanin Somaliya da Habasha."

Babban fatan Ankara shi ne samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin Somaliya da Habasha "a wannan yanki muhimmin yanki" na Afirka, in ji shi.

Turkiyya ta yi imanin cewa, yarjejeniyar hadin gwiwa da kasashen Somaliya da Habasha suka amince da ita, za ta kafa tushe mai karfi na hadin gwiwa da wadata bisa mutunta juna.

Shugaban Somaliya, Mohamud ya yaba da kokarin da Turkiyya ke yi na warware rikicin yankin iyaka da kuma sabanin siyasa da aka dade ana yi tsakanin Somaliya da Habasha, ya kuma kara da cewa kasarsa ta kasance kuma za ta ci da kasancewa "kawar Habasha ta gaskiya” a ko da yaushe.

Firaministan Habasha Ahmed ya kuma yaba da kokarin Turkiyya inda ya kira tattaunawar zaman lafiya da Ankara ta shirya a matsayin "tattaunawar iyali" wacce ta samar da sakamako mai nasara ga kasarsa da ma makwabciyarta Somalia.

A cewar sanarwar Ankara, bangarorin biyu sun yanke shawarar fara tattaunawa kan batutuwa, tare da taimakon Turkiyya, zuwa karshen watan Fabrairun 2025, tare da kammala su cikin watanni hudu.

Bangarorin biyu sun kuma tabbatar da mutunta ‘yancin Somaliya tare da fahimtar alfanun da Habasha za ta iya samu daga amintacciyar hanyar shiga teku.

Rikicin Habasha da Somaliya

Dangantaka tsakanin Habasha da Somaliya ta kara tabarbarewa bayan da kasar Habasha ta kulla yarjejeniya da yankin Somaliland mai ballewa a ranar 1 ga watan Janairu kan amfani da tashar jiragen ruwanta dake birnin Berbera.

Turkiyya dai na kokarin kawo karshen takun saka tsakanin kasashen biyu.

Habasha ta yi asarar tashoshin jiragen ruwanta a Bahar Maliya a farkon shekarun 1990 bayan yakin 'yancin kai na Eritriya, wanda aka yi daga 1961 zuwa 1991.

A shekarar 1991, Eritrea ta sami 'yancin kai daga Habasha, wanda ya kai ga kafa kasashe biyu daban-daban. Rabuwar ta sa Habasha ta rasa hanyar shiga tekun Bahar Maliya kai tsaye da kuma manyan tashoshin jiragen ruwa.

Tun dagda lokacin Habasha ta kasance ba ta da ruwa, abin da ke shafar yadda take gudanar da harkokin kasuwancin teku mai inganci.

TRT World