Tsohon shugaban kasar Tanzaniya Ali Hassan Mwinyi ya rasu.
Mwinyi, wanda ya zama shugaban ƙasa na biyu a ƙasar ta Gabashin Afirka daga 1985 zuwa 1995, ya rasu ne a ranar Alhamis, in ji shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu.
"Tsohon shugaban ƙasar Ali Hassan Mwinyi ya rasu ne a Asibitin Emilio Mzena da ke Dar es Salaam, inda yake jinyar cutar daji ta huhu," in ji Shugaba Samia a cikin wata sanarwa.
Shugaban kasar Tanzaniya Ali Hassan Mwinyi ya rasu yana da shekaru 98 a duniya.
Kafin ya hau kujerar shugaban kasa, Mwinyi ya yi aiki a matsayin malamin makaranta.
Mukamai da dama na ministoci
Tsohon shugaban kasar ya kuma riƙe muƙaman ministoci da dama da suka hada da harkokin cikin gida da kiwon lafiya da albarkatun kasa.
Ya zama jakadan Tanzaniya a Masar daga shekarar 1977 zuwa 1982.
A cikin 1984, an zaɓe shi a matsayin shugaban Tsibirin Zanzibar mai cin gashin kanta kuma mataimakin shugaban Tanzaniya.
Shugaban Tanzaniya na farko Julius Nyerere ya yi ritaya a watan Oktoban 1985 sannan ya zabi Mwinyi a matsayin magajinsa.