Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya umarci Ma’aikatar Shari’ar ƙasar da ma waɗanda ke da hannu a tsara daftarin ƙudurorin sabbin dokokin harajin da ke janyo ce-ce-ku-ce su yi aiki da majalisar dokokin ƙasar domin gyara ɓangarorin dokokin da mutane ke jin tsoro.
Wata sanarwar da ministan watsa labaran ƙasar, Mohammed Idris, ya fitar ta ce gwamnatin tarrayyar Nijeriya na maraba da duka shawarwarin da za su iya ƙarin haske game da duk wani ɓangare na daftarin dokokin da ka iya shige wa mutane duhu.
“Kazalika yana da muhimmanci a sani cewa labaran ƙarya masu yawa na yawo game da daftarin ƙudurorin haraji da ma manufar gyare-gyaren gwamnatin Tinubu. Gyare-gyaren ba za su talauta ko wace jiha ko yankin ƙasar ba kuma ba za su sa a soke ko wace hukumar gwamnatin tarraya ba,” in ji sanarwar.
“Maimakon hakan, gyare-gyaren za su kawo sauƙi ne ga miliyoyin ‘yan Nijeriya masu aiki tuƙuru a fadin ƙasar tare da ƙarfafa da kuma saka jihohinmu da kuma ƙananan hukumomi 774 a turbar ci-gaba mai ɗorewa,” a cewar ministan.
Mohammed ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu yana gyare-gyare a ɓangaren kuɗi ne ta yadda za a mayar da kuɗade da yawa hannun jihohi da ƙananan hukumomi inda kuɗaden za su koma ga mutane ta yadda za a samar da dimokuraɗiyya mai yi wa mutane aiki.
“Waɗannan gyare-gyaren ba ƙarin kuɗin shiga za su kawo wa gwamnati ba kawai (ba tare da ƙara wa mutane nauyin haraji ba), za su sa ‘yan ƙasa su iya neman bayanai game da yadda ake kashe kuɗaɗensu daga duk matakan gwamnati,” in ji sanarwar.
“Shugaba Tinubu da gwamnatin za su ci gaba samar da manufofin da za su rufe hanyoyin da aka yi ta ɓarnatar da kuɗaden Nijeriya cikin gomman shekarun da suka gabata,” a cewarsa.
Ministan ya ce Shugaba Tinubu zai ci gaba da aiki domin kare muradun 'yan Nijeriya.
“Bisa wannan muhimmin tubulin, kuɗaɗen da ake samu daga waɗannan gyare-gyaren za a saka su wajen samar da muhimman ababen more rayuwa (kiwon lafiya da ilimi da sufuri da fasahar zamani da sauransu),” in ji sanarwar.
Daftarin ƙudurorin dokar haraji dai na ci gaba da jan hankali jama’a a Nijeriya inda ake tafka muhawara game da irin tasirin da zai yi idan ya zama doka.