Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarni kan an haramta sayen motoci masu amfani da fetur a koma sayen masu amfani da gas ga ma'aikatu da hukumomin gwamnati.
Shugaban ya bayyana haka ne a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya wanda aka gudanar a ranar Litinin, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelele ya fitar ta ce.
Shugaban ya ce ya bayar da wannan umarnin ne a yunƙurin ƙasar na komawa amfani da makamashi maras gurɓata muhalli inda sanarwar ta ce an gano gas ɗin CNG ba ya fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli kamar fetur.
"Wannan ƙasar ba za ta samu ci gaba ba idan muka ci gaba rawa a wuri guda. Muna da burin aiwatar da amfani da CNG a faɗin ƙasa, kuma dole mu kafa misali da jami'an gwamnati domin su nuna hanyar makoma mai kyau ga mutanenmu. Hakan zai fara da mu, idan aka ga
Haka kuma shugaban ya bayar da umarni kan a yi watsi da duk wata takarda wadda aka gabatar a gaban Majalisar Zartarwar ta Tarayya wadda ke buƙatar a sayi motoci masu amfani da fetur.
Matakin na Shugaba Tinubu na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun wahalar man fetur a Nijeriya.
A kwanakin baya ne gwamnmatin ta Tinubu ta cire tallafin man fetur a ƙasar, wandahakan ya sa farashin fetur ɗin ya ƙaru matuka a ƙasar.