Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya gode wa kasar Faransa bisa alkawarin dawo wa kasarsa da dala miliyan dari da hamsin da tsohon shugaban mulkin sojin kasar Janar Sani Abacha ya sace.
Shugaban ya bayyana haka ne ranar Juma’a lokacin da Ministar Harkokin Wajen Faransa Catherine Colonna ta kai masa ziyara a fadarsa da ke Abuja, kamar yadda gidan talbijin na kasar NTA, ya rawaito.
Kazalika shugaban kasar ya yaba wa Faransa bisa sanya hannu kan yarjejeniya ta €100m tsakanin kasashen biyu a game da shirin i-DICE — wato shirin gwamnatin Nijeriya na zuba jari a harkokin sadarwa da fasaha da kuma kirkira.
A gefe guda, Faransa ta sha alwashin bai wa kungiyar ECOWAS karin tallafi domin ganin ta dawo da mulkin dimokuradiyya a Yammacin Afirka.
A yayin ganawarta da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Tuggar a Abuja, Colonna ta ce sun tattauna kan yadda Faransa za ta taimaka wa ECOWAS don dawo da mulki a Mali, Burkina Faso da Nijar.
"Mun ga cewa ba a mutunta jadawalin komawa tsarin mulkin dimokuradiyya kuma mun ga yadda, abin takaici, matsalar rashin tsaro ke kamari," in ji ta.
"Ya kamata mu kara azama kuma za mu taimaka wa kokarin da ECOWAS ke yi," a cewar Ministar Harkokin Wajen Faransa.
A nasa bangaren, Yusuf Tuggar, ya ce kasashen biyu sun tattauna kan zuba jari da musayar dalibai da kuma shawo kan matsalolin da suka addabi duniya.