Maryam Shetty tana cikin matasan da suka yi gwagwarmaya yayin yakin neman zaben Nijeriya na 2023./Hoto: Facebook/Maryam Shetty

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya janye Maryam Shetty daga cikin mutanen da ya mika sunayensu ga 'yan majalisar dattawan kasar domin ya nada su ministoci.

Shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a zaman da majalisar ta yi ranar Juma'a.

Ya ce Shugaba Tinubu ya tura musu sunan Dr. Mariya Mairiga Mahmoud Bunkure don maye gurbin Maryam Shetty.

Bai bayyana dalilin da ya sa shugaban kasar ya janye sunan ta ba.

Mariya Mahmoud Bunkure tsohuwar Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi ce a gwamnatin tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Mariya Bunkure kwararriya ce a fannin ilimi./Hoto:OTHER

Kazalika shugaban majalisar dattawan ya ce an mika musu sunan fitaccen lauyan nan Festus Keyamo domin a nada shi minista.

TRT Afrika