Shugaba Tinubu ya shaida cewa Nijeriya na fuskantar barazana daga makiya "mugayen makiya". / Hoto: AFP

Shugaban Nijeriya a ranar Litinin ya lashi takobin gudanar da bincike mai tsauri kan kashe farar-hula kusan 100 da sojojin kasar suka yi bisa kuskure a Kaduna da ke arewacin kasar.

Bola Tinubu ya sanar da hakan ne a wurin bude taron kwana uku na kwamandojin sojin Nijeriya da manyan jami’an sojin kasar wanda ake yi a birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Nijeriya. “Abin da ya faru a Kaduna bala’i ne babba.

Lamari ne mai ciwo a ga wani abu ya fada kan wadanda muka rantse kan cewa za mu ba su kariya.

Dole a yi kwakkwaran bincike kan irin wadannan lamuran,” kamar yadda Shugaba Tinubu ya shaida wa hafsoshin tsaron kasar da kuma kwamandojin sojin kasar.

Ya bayyana cewa za a gudanar da wannan binciken ne domin tabbatar da cewa sojojin ba su sake gudanar da irin wannan kuskuren a gaba ba.

A ranar 3 ga watan Disamba ne jirgi maras matuki ya kai hari a kauyen Tudun Biri inda sojojin kasar suka ce an kai harin ne a bisa kuskure.

Tinubu ya bukaci sojojin kasar da su mayar da hankali wurin hada kai da sauran jami’an tsaro domin magance matsalar ta’addanci, da fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran laifuka domin Nijeriya ta samu ci gaba.

“Rayuwar kasarmu na hannun jami’an tsaronmu,” kamar yadda ya bayyana. Ya kuma ce Nijeriya na fama da “mugayen makiya” wadanda suke so su kawo cikas ga dimokuradiyyar kasar da kuma zaman lafiya.

AA