Shugaban Nijeriya Bola Tinubu a ranar Laraba ya bukaci majalisar dattawan kasar ta amince ya ciyo bashin kusan dala biliyan 8 a wani bangare na sabon bashin ketare na shekarar 2022-2024 don yin ayyukan raya kasa da kiwon lafiya da ilimi da kuma tsaro.
Nijeriya ce kasar Afirka mafi karfin tattalin arziki kuma ita ce ta daya a hako man fetur, sai dai ta dogara ne a kan bashi saboda yadda ba ta iya tattara haraji da kuma yadda ta rage fitar da danyen man fetur zuwa ketare, wanda shi ne babbar hanyar da take samun kudin kasahen kasashen waje.
A wata wasika da ya aika wa majalisar dattawa, Shugaba Tinubu ya bukaci dala biliyan 7.86 da yuro miliyan 100, sai dai bai yi karin haske ba kan yadda za a samo kudin.
Nijeriya ta samu kudi daga ketare ta hanyar takardun lamuni na Eurobond da kuma rance daga Bankin Duniya da Bankin Ci-gaban Afirka don cike gibin kasafin kudinta.
Karfafa gwiwar masu zuba jari
"Bisa la'akari da halin tattalin arzikin da ake ciki yanzu a kasar, ya zama wajibi a ciyo bashi daga ketare don cike gibin kudi da za a yi amfani da su wajen ayyuka masu muhimmanci kamar fannin wutar lantarki da jirgin kasa da kiwon lafiya da sauransu," in ji Tinubu.
Gwamnatinsa ta ce tana so ta karfafa wa masu zuba jari gwiwa maimakon ta dogara kan karbo bashin kudi wajen samar da ayyuka yi da kuma yin manyan ayyukan raya kasa.
Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai suna duba yiwuwar yin karamin kasafin kudi na naira tiriliyon 2.176 (kimanin dala 2.8 kenan) don yin wasu "ayyuka na gaggawa" ciki har da wasu ayyuka a fannin tsaro.
Mako biyu da suka wuce majalisar zartarwar Nijeriya ta amince da naira tiriliyan 26.01 (dala biliyan 34) a matsayin kasafin kudin shekara mai zuwa na ksar, wanda aka ware kusan daya bisa uku na adadin wajen biyan kudin ruwa. Kimanin kaso 40 cikin 100 na jumullar bashin da ake bin Nijeriya na kasashen ketare ne.