Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce ya bai wa hedkwatar tsaro da shugaban rundunar tsaron ƙasar "cikakken iko" na hukunta duk wanda aka samu da laifin kisan wasu sojoji a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.
Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi domin jin ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan sojojin da goma sha shida wasu matasa suka kashe a ƙaramar hukumar Ughelli ta jihar Delta ranar Alhamis ɗin da ta gabata.
Sojojin waɗanda suka haɗa da kwamanda ɗaya da masu muƙamin manjo guda biyu da kyaftin ɗaya da kuma ƙananan sojoji 12 sun rasu ne a yayin da suka kai ɗauki wurin wani rikicin ƙabilanci a ƙauyen Okuama.
"Ranar Asabar da safe, ƴan Nijeriya da ni mun wayi gari da samun baƙin labari na kisan zaratan sojojinmu da ba su ji ba, ba su gani ba yayin da suka je ƙauyen Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli South a jihar Delta domin ƙai ɗauki," in ji Shugaba Tinubu.
Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne lokacin da aka yi wa sojojin kwanton-ɓauna. "Abin baƙin ciki shi ne Kwamanda ɗaya da masu muƙamin manjo guda biyu da kyaftin ɗaya da kuma ƙananan sojoji 12 sun rasu. Haka kuma an kashe farar-hula guda ɗaya".
Shugaban na Nijeriya ya ce "matsorata" ne suka yi wannan ɗanyen-aiki, yana mai cewa gwamnatinsa ta bai wa Hedkwatar tsaro da shugaban rundunar tsaron Nijeriya "cikakken iko" su hukunta duk wanda aka samu da laifi a kan mutanen Nijeriya.
Shugaba Tinubu ya ce "sojojinmu su ne ginshiƙin gina ƙasarmu. Duk wani hari da aka kai musu, hari ne a kan ƙasarmu kai-tsaye. Ba za mu amince da wannan ƙeta ba."
"Ina mika ta'aziyyata ga iyalan waɗannan sojoji da aka kashe da abokan aikinsu da masoyansu. Tuni rundunar tsaro ta soma mayar da martani kan wannan lamari. Matsorantan da suka yi wannan ɗanyen-aiki ba za su ci bulus ba," a cewar Shugaba Tinubu.
Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta gajiya ba har sai an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowanne ɓangare na Nijeriya.