Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata a Nijeriya

Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata a Nijeriya

Mohammed Idris, Ministan Watsa Labarai Mohammed Idris ne ya sanar da hakan a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis.
Mohammed Idris, Ministan Watsa Labarai Mohammed Idris ne ya sanar da hakan a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan ƙasar, inda ya yi alkawarin za a dinga nazarin mafi ƙarancin albashin duk bayan shekara uku.

Mohammed Idris, Ministan Watsa Labarai Mohammed Idris ne ya sanar da hakan a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Minista Idris ya ce Shugaban Ƙasar ya sanar da hakan ne a taron da ya yi da shugabannin ƙungiyar Ƙwadago na ƙasar.

“Muna farin cikin sanar da ku a yau (Alhamis) cewa kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya sun amince da karin albashin N62,000. Sabon mafi karanci na kasa da ake sa ran Shugaban Ƙasa zai miƙa wa majalisar kasa shi ne ₦70,000,” in ji Idris.

Shugaban NLC Joe Ajaero da shugaban TUC, Festus Osifo da Ministan Ƙwadago Nkiruka Onyejeocha, da sauran jami’an bangarorin biyu sun tabbatar da batun ninistan.

Yarjejeniyar tsakanin bangarorin biyu ta biyo bayan wasu jerin tattaunawa tsakanin shugabannin kwadago da shugaban kasar a ‘yan makonnin da suka gabata, bayan da aka shafe watanni ana tattaunawar da aka gaza cimma matsaya tsakanin ɓangarorin uku na kwamitin mafi karancin albashi da shugaban kasar ya kafa a watan Janairu.

Kafin sanarwar ƙrin a ranar Alhamis, mafi ƙrancin albashi a Nijeriya Naira 30,000 ne. Amma a musayar ra'ayoyin da aka dinga yi kan ƙarin, ƙungiyoyin ƙwadago sun nemi gwamnati ta mayar da shi Naira 250,000 saboda hauhawar farashi da tsadar rayuwa da ake fama da su a ƙasar.

TRT Afrika