Yawan bidiyoyin da aka goge kashi ɗaya ne kawai a cikin gaba ɗaya bidiyoyin da aka wallafa daga Nijeriya a tsakanin wannan lokaci. Tiktok / Hoto: Reuters

Kamfanin Tiktok ya ce ya goge bidiyoyi fiye da miliyan 2.1 a Nijeriya daga watan Afrilu zuwa Yunin 2024 saboda take dokokinsa.

A cikin rahoton dokokinsa da ya fitar a ranar Talata, Tiktok ya ce ya ɗauki wannan mataki ne a ƙoƙarin kamfanin na ci-gaba da bunƙasa kula da abubuwan da ake wallafawa kuma samar da yanayi mai aminci ga masu amfani da shafin.

Muhimman bayanai daga rahoton sun nuna an goge cewa kashi 99.1 cikin 100 na bidiyoyin tun ma kafin masu amfani da shafin su miƙa ƙorafi a kansu, inda aka goge kashi 90.7 cikin 100 a cikin awa 24.

Rahoton kamfanin ya ce waɗannan alƙaluma suna nuna jajircewar Tiktok na magance abubuwan da ke da illa da cutarwa da kuma tabbatar da samar da ingantacciyar ƙwarewa ga masu amfani da shafin a Nijeriya.

Yawan bidiyoyin da aka goge kashi ɗaya ne kawai a cikin gaba ɗaya bidiyoyin da aka wallafa daga Nijeriya a tsakanin wannan lokaci.

A mataki na duniya kuwa, Tiktok ya goge bidiyoyi miliyan 178 a watan Yunin 2024, inda na’ura ta goge miliyan 144 kai tsaye bayan gano suna da illa.

Ta hanyar amfani da ƙwarewa wajen gano saɓa dokoki da ya kai matakin kashi 98.3 cikin 100 a fadin duniya, a yanzu Tiktok ya fi daukar matakan da suka dace wajen hana watsa bidiyoyi masu illa tun kafin su isa ga masu amfani da manhajar, in ji kamfanin.

Bugu da ƙari, TikTok ya ƙarfafa ƙudurinsa na nuna gaskiya da amincin dandalin ga mutane daban-daban da ke amfani da shi a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

TRT Afrika