A ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu na 2024 gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake naɗa Muhammadu Sanusi na II sarautar Kano, shekaru fiye da huɗu bayan tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya sauke shi daga sarautar.
Gwamnan ya sanar da sake naɗa Muhammadu Sanusi II kan sarautar Kano ne a wani jawabi da ya yi wa al'ummar jihar kai-tsaye, jim kadan bayan ya sa hannu kan gyaran dokar Masarautun Kano ta 2024 da majalisar dokokin jihar ta yi da safiyar Alhamis.
Ya ce wannan mataki na nufin a yanzu jihar Kano tana da "Sarki ɗaya tilo."
Tun da farko, Majalisar Dokokin Jihar ta soke masarautu biyar da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙira a 2019 sannan ta naɗa musu sarakuna masu daraja ta ɗaya, tana mai cewa an yi hakan ne ba bisa ƙa'ida ba.
Masarautun da aka soke su ne: Birnin Kano, Gaya, Rano, Bichi da Ƙaraye.
Wane ne Muhammadu Sanusi II?
- An haife shi a tsatson sarakunan Fulani a ranar 31 ga watan Yuli 1961.
- Jika ne ga sarki Sanusi da aka sauke daga gadon sarauta.
- Ya samu digiri a fannin Tsimi da Tanadi da fannin Addini Musulunci - a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da kuma Ƙasar Sudan.
- Tsohon shugaban Nijeriya Umaru YarAdua ya naɗa shi muƙamin gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) a watan Yuni na 2009.
- Mujallar Banker ta bayyana shi a matsayin gwarzon shekara a 2010.
- Gwamnatin tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ta dakatar da shi daga gwamnan a watan Fabrairu
- An naɗa shi a matsayin Sarkin Kano ranar 8 ga watan Yuni 2014.
- Tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya sauke shi daga sarautar Kano ranar 9 ga watan Maris na 2020
- Ya zama Khalifan Ɗariƙar Tijjaniyya na Nijeriya a shekarar 2021.