Babban jami’in diflomasiyya na Tarayyar Turai ranar Litinin ya bayyana goyon bayansa ga jakadan Faransa a Nijar, wanda yake fuskantar matsin lamba bayan ya ki fita daga kasar duk da korar da sojojin da suka yi juyin mulki suka yi masa.
Bayan kifar da gwamnatin da aka zaba a watan Yuli, sojojin sun kori Jakada Sylvain Itte, amma Faransa ba ta yarda da sahihancin mulkin su ba.
Shugaba Emmanuel Macron a makon jiya ya ce “an yi gakuwa” da jakadan nasa a ofishin jakadancin kasar, bayan da aka dakatar da kayan da sojoji suke shiga da su.
"Muna goyon bayan Faransa game da halin da jakadanta yake ciki," in ji jami’in tsare-tsaren kasashen waje na Tarayyar Turai Josep Borrell a hirarsa da manema labarai a gefen wurin Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a New York.
Ya jaddada cikakken goyon bayan Tarayyar Turai ga "Mohamed Bazoum, zababben shugaban kasa wanda sojoji suke tsare da shi”, sannan ya jinjina masa bisa “zage dantse da jajircewarsa."
Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun umarci 'yan sanda su fitar da jakadan Faransa daga kasar
Borrell ya ce Turai ta amince da bukatar “sake nazari” game da tsare-tsarenta a yankin Sahel, inda Faransa ta kwashe shekara da shekaru tana yaki da masu ikirarin jihadi.
"Muna bukatar sabon tsari saboda muna fuskantar yanayi mai sarkakiya," in ji shi.
"Mun amince cewa Afirka ce ya kamata ta magance matsalar da ke addabarta."
A cikin shekaru fiye da goma, Tarayyar Turai ta kashe sama da euro miliyan 600 a harkokin farar-hula da na soji a yankin Sahel, inda ta bayar da horo ga fiye da jami’an tsaro 30,000 da kuma sojoji 18,000 na kasashen Mali da Nijar, in ji Borrell.
Amma duk da haka sojoji sun yi juyin mulki a kasashen biyu, da ma makwabciyarsu Burkina Faso.