US African Union / Photo: AP

Tarayyar Afirka ta bayyana “matukar damuwa” game da rikici a Kenya, biyo bayan zanga-zanga kan tsadar rayuwa a kasar.

Akalla mutum daya ne ya rasa ransa yayin bata kashi tsakanin masu zanga-zanga da ‘yan sanda a babban birnin kasar na Nairobi.

Shugaban ‘yan adawa, Raila Odinga ya yi kira da a dinga gudanar da zanga-zanga duk kowace Litinin da Alhamis.

A ranar Litinin, daruruwan mutane sun far wa gonar tsohon shugaban kasar UhuruKenyatta, wadda take wajen birnin Nairobi, a inda suka wawashe dabbobi kuma suka sare bishiyoyi.

A wata sanarwa, shugaban kwamitin Gudanarwar Tarayyar Afirka Moussa Faki, ya nemi “duka masu ruwa da tsaki su kai zuciya nesa, kuma su hau teburin tattaunawa” domin abin da ya kira da “gagarumar manufar hadin-kan kasa da sasantawa”.

Mr. Faki ya bayyana cewa “zanga-zangar al’umma kan haifar da rasa rayuka da barnata dukiyoyi da tarnaki ga harkokin tattalin arziki”.

Haka nan ya sanar da kudurin Tarayyar Afirka na “cikakken” goyon baya ga gwamnati da mutanen Kenya a yunkurinsu na kawo “hadin kan kasa da zaman lafiya a kasar”.

Shugaban ‘yan adawa Raila Odinga ya yi tir da wawason da aka yi wa gonar tsohon shugaba, Kenyatta. Amma ya sha alwashin ci gaba da zanga-zanga da suke kan tsadar rayuwa a kasar.

TRT Afrika