Rwanda da Hukumar Tarayyar Afirka da Hukumar Kula da ‘yan Guduj Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya sun amince su tsawaita yarjejeniyar karɓar ‘yan Afirka masu gudun hijira da suka maƙale a Libya.
Yarjejeniyar ta fahimtar juna da aka sanya wa hannu a watan Satumbar 2019, za ta ci gaba da aiki har zuwa 31 ga Disambar 2025, kamar yadda wata takardar sanarwa da ɓangarorin biyu suka sanya wa hannu a ranar Juma’a ta nuna.
“Yarjejeniyar ta jaddada aniyar ɓangarorin biyu ta samar da kariya da neman mafita mai ɗorewa ga ‘yan gudun hijira da masu neman mafaka da aka fitar da su daga Libya,” a cewarta.
Ta ce tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, an kwashe fiye da ‘yan gudun hijira da masu neman mafaka 2,300 daga Eritrea da Sudan da Sudan ta Kudu da Somalia da Ethiopia da Nijeriya da Chadi da Kamaru da Guinea da Cote d’Ivoire da kuma Mali.
‘Ci gaba da ba da kariya’
Lokacin da aka sanar da matakin a 2019, Rwanda ta shirya karɓar ‘yan Afirka kimanin 30,000 daga Libya.
Sanarwar ta ƙara da cewa Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta MDD za ta “ci gaba da samar da kariya da agajin da ake buƙata, da suka hada da wuraren zama da abinci da kiwon lafiya da sauran kayan bukatun yau da kullum ga mutanen da aka kwaso, iya zaman da za su yi a Rwanda.”
Libya na yukurin farfaɗowa daga shekarun da aka shafe ana rikici, bayan boren da aka yi a 2011 wanda NATO ta goyawa baya, ya hamɓarar da Shugaba Mu’ammar Gaddafi, sannan kasar ta zama a rabe tsakanin gwamnatin da Majalisar Ɗinkin Duniya take goyawa baya da ke zaune a birnin Tripoli da kuma masu adawa da ita da ke gabashin ƙasar.
A wannan watan, MDD ta nuna damuwa kan yadda al’amuran tsaro da tattalin arziki ke kara taɓarɓarewa a Libya.