Cutar ta samo asali ne daga jemage. Photo AP

Gwamnatin Tanzaniya ta tabbatar da cewa babu sauran mai cutar Marburg a kasar, inda ta ce a halin yanzu za a iya kai ziyara kasar lami lafiya.

Sanarwar da ma’aikatar da ke kula da albarkatun kasa da yawon bude ido ta fitar a ranar Litinin na zuwa ne bayan da kasar ta sanar da barkewar cutar a karon farko a watan da ya gabata, inda ta kashe mutum biyar a arewa maso yammacin yankin Kagera.

Akalla mutum 161 aka tabbatar da suna cikin hatsarin cutar, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar.

“Muna so mu tabbatar wa bakinmu cewa Tanzaniya ba ta cikin hatsari kuma kasa ce da ke maraba a kullum.

"Muna iya bakin kokarinmu domin tabbatar da cewa bakinmu sun ji dadin zuwan da suka yi hankali kwance,” in ji ministan kula da albarkatu da yawon bude ido Mohamed Mchengerwa.

Duk da cewa ba a samu labarin cutar Marburg a wani wurin yawon bude ido ba, amma sanarwar ta ce hukumomi a yankunan sun dauki matakai kuma za a ci gaba da sa ido.

Cutar Marburg wadda tana daga cikin cututtuka irin su Ebola, na jawo zazzabi mai zafi, kuma an soma gano ta ne a 1967 a Marburg da Frankfurt da ke Jamus da kuma Belgrade da Serbia.

Adadin mutuwa kan cutar yana daga kashi 24 cikin 100 zuwa 88, inda barkewar cutar mafi muni ta faru ne tsakanin 2004-2005 inda mutum 252 suka kamu sai kuma 227 suka rasu.

Asali cutar jemage ne ke yada wa bil adama daga nan sai ta yadu ta hanyar ruwan jikin mutane, inda ma’aikatan lafiya da kuma iyalan wadanda suka kamu suke zama wadanda suka fi hatsarin kamuwa.

Alamomin cutar sun hada da zazzabi da amai da kuraje inda cikin kwanaki 21 cutar ke tasiri.

TRT Afrika da abokan hulda