Kungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka ta ce a ranar Juma'a ta soke shirin tattaunawa da shugabannin sojoji a Nijar ne saboda matsalar da wani jirgin da aka yi hayarsa ya samu.
Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta ƙaƙabawa Nijar takunkumi mai tsauri tun bayan juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023, amma tana kokarin yin tattaunawa don gani an koma mulkin farar hula.
A ranar Alhamis ne Firaministan da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta nada ya soki kungiyar ECOWAS da "yaudara" bayan da kowa ya ƙi halartar tsaron da aka tsara sai Ministan Harkokin Wajen Togo kadai.
“Tawagar al’ummar yankin sun shafe tsawon yini Alhamis a filin jirgin sama da ke Abuja, sun shirya domin tashi zuwa Yamai,” in ji ECOWAS a cikin wata sanarwa.
Technical problems
"Abin takaici, jirgin da ƙungiyar ta yi hayarsa don tashi daga Abuja zuwa Yamai ya samu matsala."
Kungiyar ECOWAS ta ce za ta sake saka sabuwar ranar yin taron ba tare da ɓata lokaci ba.
Shugabannin Nijar dai sun yi fatan tattaunawa da ƙasashen ECOWAS don warware matsalolin da ke tsakaninsu..
Tun bayan juyin mulkin, ECOWAS ta dage cewa dole ne a saki Bazoum daga tsare shi da ake yi idan har ana so a janye takunkuman da aka ƙaƙaba mata, sannan kuma shugabannin sojoji sun amince da a miƙa mulki ga farar hula a taƙaice.
Shiga tsakani
A ranar 8 ga watan Janairu aka sako ɗan Bazoum, Salem, wanda da farko aka tsare shi tare da iyayensa, kuma ya tafi Togo, ƙasar da Ministan Harkokin Wajenta Robert Dussey ke neman shiga tsakani da gwamnatin juyin mulkin.
Gwamnatin Nijar ta ce tana shirin miƙa mulki ga gwamnatin farar hula bayan shekaru uku, sannan da shiga shekarar 2024 sai ta fara matsa ƙaimi ga tattaunawar yankin gabanin tattaunawar ƙasa game da taswirar miƙa mulki.