| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Taiwo Akinkunmi: Mutumin da ya zayyana tutar Nijeriya ya rasu
Mista Akinkunmi shi ne ya tsara yadda tutar Nijeriya za ta kasance tun lokacin samun 'yancin kai.
Taiwo Akinkunmi: Mutumin da ya zayyana tutar Nijeriya ya rasu
Akinwumi ya rasu yana da shekara 87. Hoto/Others / Others
30 Agusta 2023

Mutumin da ya zayyana tutar Nijeriya, Taiwo Akinkunmi ya rasu yana da shekara 87.

Dansa Akinkunmi Akinwumi Samuel ne ya sanar da mutuwar mahaifin nasa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

Ya rubuta cewa, “Rayuwa da gaske ba ta da yawa; zan iya fada karara cewa ka yi rayuwa mai tarihi. Ka ci gaba da hutawa, mahaifina! Pa Michael Taiwo Akinkunmi (O.F.R) Babban mutum ya tafi”, in ji dan nasa.

Akinkunmi wanda dan Jihar Ogun ne daga kudancin Nijeriya, ya yi rayuwa a birnin Ibadan har zuwa rasuwarsa.

Ya soma aikin gwamnati ne a Ibadan inda daga baya ya tafi kasar Norway domin karantar kimiyyar aikin gona.

A 1958, a lokacin da yake zama a waje, sai Akinkunmi aka ce ya ga talla a jarida wadda take neman a zayyana sabuwar tutar Nijeriya gabannin samun ‘yancin kai.

Alkalai wadanda suka yi alkalanci sun zabi tasa a cikin kusan 2,000 wadanda aka zayyana.

An soma amfani da tutar ne a ranar 1 ga watan Oktobar 1960.

MAJIYA:TRT Afrika