Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce zai kwashe dakarun kasar daga Nijar nan da karshen shekarar da muke ciki / Hoto: DPA

Jakadan Faransa a Jamhuriyar Nijar ya fice daga kasar da sanyin safiyar Talata, a cewar wasu majiyoyin tsaro da diflomasiyya guda biyu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

Jakadan ya bar Yamai ne kusan wata guda bayan sojojin da suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum sun ba shi wa'adin awa 48 ya fita daga kasar.

A watan jiya ne sojojin kasar suka bai wa Jakada Sylvain Itte umarnin fita daga kasar bayan "ya ki amsa gayyatar ma'aikatar harkokin waje don halartar taron" da aka gayyace shi da kuma "wasu matakai da Faransa ta dauka da suka ci karo da muradan Nijar".

Sai dai da farko shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce jakadan ba zai fita daga Nijar ba sannan ya yi zargin cewa sojojin kasar sun yi "garkuwa" da shi.

Amma a ranar Lahadin da ta gabata Mr Macron ya ce Faransa za ta janye jakadanta da kuma sauran ma'aikatan jakadanci cikin awanni kadan.

Labari mai alaka: Faransa za ta kwashe dakaru da ma'aikatan jakadancinta daga Nijar: Macron

Kazalika ya ce za su kwashe dakarunsu 1,500 da ke Nijar watanni biyu bayan takaddama ta ki ci ta ki cinyewa tsakaninsa da sojojin kasar kan juyin mulkin da suka yi.

Faransa ta ki amincewa da sabuwar gwamnatin sojin Nijar kuma Macron ya ce har yanzu kasarsa tana kallon Bazoum a matsayin halastaccen shugaban kasa, yana mai yaba masa kan kin mika wuya ga sojojin.

Tun bayan juyin mulkin, sojojin sun soke kawancen tsaro da ke tsakaninsu da Faransa sannan suka umarci jakadanta ya fita daga kasar bayan sun soke izininsa na zama a Nijar.

Macron ya ce yana so ya janye 'yan kasar tasa daga Nijar cikin lumana. Ranar Litinin sojojin Nijar sun ce suna so a tsara jadawalin ficewar dakarun Faransa daga kasar.

TRT Afrika da abokan hulda