Hamdok

Ma'aikatar Lafiyar Sudan ta ce rikicin da ake yi tsakanin dakarun soji da rundunar Rapid Support Forces [RSF] ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 528 kawo yanzu.

Ta bayyana haka ne a yayin da tsohon firaiministan kasar Abdalla Hamdok ya yi gargadin cewa Sudan na cikin kasadar fadawa yakin-basasa, yana mai cewa muddin hakan ya faru, yake-yaken da ake yi a Syria, Yemen da Libya za su zama tamkar wasan yara bisa abin da zai faru a kasarsa.

Wata sanarwa da ma'aikatar lafiyar kasar ta fitar ranar Asabar ta kara da cewa an jikkata mutum akalla 4,599 sakamakon rikicin da ya barke ranar 15 ga watan Afrilu.

Ta ce rikicin ya watsu zuwa jihohi 12 cikin 18 lamarin da ka iya ta'azzara.

Kazalika fadan ya raba mutum 75,000 daga muhallansu a Khartoum da jihohin Blue Nile da North Kordofan, da ma yankin Darfur, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Da ma dai Sakatare Janar na Majalisar, Antonio Guterres, ya yi gargadin cewa Sudan tana kan turbar wargajewa sakamakon rikicin.

"Babu wani amfanin neman mulki a kasar da take wargajewa," in ji Mr Guterres a hirarsa da gidan talbijin na Al Arabiya.

Rikicin, wanda ake yi tsakanin sojin da ke karkashin shugaban rundunar soji ta kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa wanda ke jagorantar rundunar RSF, Janar Mohammed Dagalo, ya kawo tsaiko ga shirin mayar da kasar kan turbar dimokuradiyya.

Rashin hankali

Abdalla Hamdok ya zama shugaban gwamnatin rikon-kwaryar kasar bayan sojoji sun hambarar da dadadden shugaba Omar al Bashir a 2019. Hoto: Reuters

Hamdok ya bayyana rikicin a matsayin wani "rashin hankali" yana mai cewa zai iya shafar dukkan duniya.

Ya bayyana haka ne a Nairobi, babban birnin Kenya a wurin taron karrama shugabanni nagari mai taken The Ibrahim Governance Weekend (IGW), wanda Gidauniyar Mo Ibrahim Foundation ta gudanar.

Abdalla Hamdok ya zama shugaban gwamnatin rikon-kwaryar kasar bayan sojoji sun hambarar da dadadden Shugaba Omar al Bashir a 2019.

Tsohon firaiministan, wanda Janar-Janar din da ke rikici yanzu suka cire daga mukaminsa a 2021, ya ce: ‘’Abin Allah ya kiyaye shi ne idan Sudan ta kai matakin da yakin-basasarta zai shafi dukkan yankin... Ina ganin hakan zai zama wani babban bala'i a duniya.”

TRT World