Ministan Shari'a Muawiya Osman ya ce a ranar Talata gwamnatin Burhan ta kai karar kasar Chadi gaban kungiyar Tarayyar Afirka.  / Hoto: AP

Sojojin Sudan da ke samun goyon bayan gwamnatin ƙasar sun zargi maƙwabciyarta Chadi da samar da makamai ga mayakan ‘yan tawaye, mai yiwuwa tana nufin dakarun sa-kai da take fafatawa da su.

Ministan Shari'a Muawiya Osman ya ce a ranar Talata gwamnatin Burhan ta kai karar kasar Chadi gaban kungiyar Tarayyar Afirka.

Da yake magana da manema labarai, ciki har da AFP, Osman ya ce gwamnati ta buƙaci a biya ta diyya, ya kuma zargi Chadi da "sayar da makamai ga mayakan 'yan tawaye" da kuma "illata 'yan kasar Sudan".

"Za mu gabatar da shaidu ga hukumomin da abin ya shafa," in ji shi daga Port Sudan, inda Burhan ya koma bayan fada ya bazu zuwa babban birnin kasar, Khartoum.

An raba fiye da mutum miliyan 11 da muhallansu

A watan jiya ne kasar Chadi ta musanta zargin da ake mata na cewa tana “kara habaka yakin Sudan” ta hanyar bai wa kungiyar RSF makamai.

"Ba ma goyon bayan wani bangare da ke yaki a kasar Sudan - muna goyon bayan zaman lafiya," in ji ministan harkokin wajen kasar kuma kakakin gwamnati Abderaman Koulamallah a lokacin.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi amfani da mashigar Adre da ke tsakanin kasashen biyu wajen kai kayan agaji.

Tun da farko Sudan ta amince ta ci gaba da bude mashigar na tsawon watanni uku, wanda zai kare a ranar 15 ga watan Nuwamba.

Hukumomin birnin Khartoum dai ba su yanke shawarar tsawaita shirin ba.

Yakin basasar Sudan ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane tare da raba fiye da miliyan 11 da muhallansu, ciki har da miliyan 3.1 da a yanzu ke mafaka a kan iyakokin kasar.

TRT Afrika