Sudan ta sanar da cewa tattaunawar da aka gudanar a birnin Jeddah na Saudiyya tare da Amurka ta kawo ƙarshe ba tare da cim ma matsaya ba kan halartar Khartoum ɗin zuwa taron zaman lafiya da za a gudanar a birnin Switzerland.
Taron na zaman lafiya wanda aka shirya gudanarwa a ranar 14 ga watan Agusta, an shirya shi domin tattauna yadda za a magance rikicin da ake yi tsakanin Rundunar Sojin Sudan da kuma ƙungiyar dakarun RSF.
Jagoran wakilan na Sudan a birnin Jeddah Mohamed Bashir Abu-Na mo ya bayyana cewa an kammala tattaunawar ba tare da cim ma matsaya ba dangane da halartar gwamnatin ta Sudan taron tattaunawar da za a yi a Geneva.
“Wannan shawara ce ga jagorori kan kada su halarci tattaunawar da za a yi a Geneva,” in ji Abu-Namos.
“A karshe dai al’amarin ya rage ga shawarar da shugabanni suka yanke, kuma tabbas akwai bayanai da dama da suka sa muka ɗauki wannan matakin na kawo karshen tattaunawar ba tare da cim ma matsaya ba,” kamar yadda ya ƙara da cewa.
Ana cikin mawuyacin hali a Sudan sakamakon rikicin da ake fama da shi tsakanin sojojin ƙasar da kuma rundunar RSF wanda hakan ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 18,800 sannan kusan mutum miliyan 10 suka rasa muhallansu