Somaliya ta sanar da cewa daga yanzu zuwa karshen watan Yunin 2024 za ta haramta amfani da robar ''take-away'' da ake zuba abinci.
Ma'aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta ce Mogadishu ta dakatar da shigarwa da fitarwa da kuma masana'antu da kasuwancin amfani da robobin -''take- away'' da ake zuba abinci a Somaliya daga ranar 30 ga watan Yuni na 2024."
Ma'aikatar ta bukaci kamfanoni da 'yan kasuwa a kasar su kirkiro da wasu hanyoyi da za su maye gurbin robobin wadanda ba za su cutar da muhalli ba.
Kazalika ma'aikatar ta ce gwamnati za ta tallafa wa ‘yan kasuwa wajen nemo kayayyakin da za su maye gurbin robobin.
Masu goyon bayan sauyin yanayi da fafutukar kare muhalli sun yi maraba da wannan mataki.
Rayuwar kasa da ta ruwa
Wakilin Somaliya a gidauniyar 'Nordic International Support Foundation' da ke tallafa wa kasashen masu fama fa tashe-tashen hankula a duniya, Kassim Gabowduale, ya ce robobin zuba abinci na ''take- away'' sun janyo barna a fadin kasar tare da jefa rayuwar muhalli ta kasa da kuma ta cikin ruwa cikin hadari.
Ya ce robobin sun zama babbar hanyar gurbatar muhalli, inda suka zama sanadin kashe dabbobin kasa da na cikin teku.
"Rashin samar da hanyoyin sarrafa shara a Somaliya musamman a manyan biranen kasar shi ne ya sa mutane ke zubar da shara yanda suka dama , musamman robobi a cikin teku," in ji shi.
Ya kara da cewa, haramcin zai rage illar da ake haifar wa kan muhalli a Somaliya.
Karkatar da hankali
''Wannan mataki ne da ta dace domin zai ceci rayuwar muhalli ta kasa da kuma ta cikin ruwa,'' in ji shi
Abdullahi A. Hassan, babban daraktan kungiyar Community Action for Climate Change (CACC), wata kungiya mai zaman kanta dake rajin sauyin yanayi, ya ce an dauki tsawon lokaci wajen kafa wannan doka saboda kalubalen da kasar ke fuskanta da kuma karancin albarkatun kasa.
"Tsawon shekariun da aka kwashe ana fama da rikice-rikice da rashin zaman lafiya wadanda suka karkatar da hankali da kuma albarkatu daga matsalolin da suka shafi muhalli," in ji shi.
Hassan ya ce rashin sanin ya kamata da kuma wayar da kan jama’a game da illar gurbatar da muhalli da robobi ke janyowa na iya kara kawo jinkirin daukar mataki.
Zuba dala miliyan 10
Sakamakon rashin nauyin robobin zuba abinci da yadda iska da ruwa ke iya tafiya da su, ya sa suke lalata birane da yankunan karkara da magudanar ruwa a Somaliya.
“Wadannan robobi suka zama shara tare da gurbata muhalliu, ciki har da rairayin bakin teku da koguna da kuma filayen noma, Robobin sun haifar da gagarumin illa ga muhalli a kasar,” in ji Hassan.
Somaliya ta dade tana aikin samar da matakai kare duk wata halitta kasar.
Shugaba Hassan Sheikh Mahamud ya yi alkawarin saka dala miliyan 10 don magance matsalar sauyin yanayi, kwararowar hamada da kuma kare rayayyun halittu a shekarar 2023.
Afirka dai na kara fuskantar matsaloli da suka shafi yanayi, kodayake tana ba da gudummawar kashi 4 cikin 100 na hayakin dake gurbata yanayi a duniya.