Somaliya na zargin makwabciyarta Habasha da samar da makamai ga yankinta na Puntland da ke arewa maso gabashin kasar, yankin da a bana ya bayyana cewa ya zama kasa mai cin gashin kai duk da rashin amincewa da gwamnatin ta Somalia ta nuna.
Akwai tarihin dambarwar dangantaka tsakanin Habasha da Somaliya.
Takun saka tsakanin kasashen yankin kusurwar Afirka ya karu ne a ranar 1 ga watan Janairu, lokacin da Addis Ababa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani yankin arewacin Somaliya - yankin Somaliland ta ya ɓalle - wanda ya bai wa kasar Habasha, wadda ba ta da teku damar samun iko da teku.
"Somaliya na Allah wadai da jigilar makamai ba tare da izini ba daga Habasha zuwa yankin Puntland na Somalia, da keta huruminmu da kuma yin barazana ga tsaron yanki," in ji ma'aikatar harkokin wajen kasar da ke Mogadishu a wata sanarwa da ta fitar a shafin X a ranar Juma'a.
"Muna bukatar dakatar da hakan da gaggawa tare da yin kira ga ƙasashe abokan hulɗa da su goyi bayan kokarin samar da zaman lafiya a yankin kusurwar Afirka."
Puntland, wanda ya kasance yanki mai ɗan cin gashin kansa na Somaliya tun shekarar 1998, ya ce a watan Janairu zai yi aiki a matsayin kasa mai cikakken cin gashin kansa, sakamakon takaddamar da ke tsakaninsa da gwamnatin tsakiya kan sauye-sauyen kundin tsarin mulkin kasar.
Jigilar makamai
A cikin sakon da ta wallafa a shafinta na X, ma'aikatar harkokin wajen Somalia ta ce: "Sahihan bayanai sun tabbatar da zuwan wasu manyan motocin daukar kaya guda biyu da ke jigilar makamai daga Habasha zuwa yankin Puntland na Somalia, lamarin da aka aiwatar ba tare da wata alaka ta diflomasiyya ko izini ba."
"Wannan aiki ya zama babban cin zarafi ga ikon mulkin Somaliya kuma yana da matukar tasiri ga tsaron kasa da na yanki."
Sanarwar ba ta bayyana lokacin da aka aika da makaman ba, ko kuma wanda aka aika wa makaman ba.
Ma'aikatar harkokin wajen Habasha ba ta amsa bukatar kamfanin dillancin labarai na AFP ba nan tak domin jin ta bakinta.