Dakarun sojin Sudan ƙarƙashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan sun kwashe watanni 16 suna fafatawa da mayaƙan rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces. / Hoto: Reuters

Shugaban mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce gwamnatinsa ba za ta shiga tattaunawar zaman lafiya da ake yi a Switzerland ba da rundunar kai ɗaukin gaggawa ta ƙasar, yana mai cewa maimakon haka za su kwashe "shekara 100 suna yaƙi."

"Ba za mu je Geneva ba... za mu kwashe shekara 100 muna yaƙi," in ji Burhan, wanda dakarunsa suka kwashe watanni 16 suna fafatawa da mayaƙan rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces. Ya bayyana haka ne ga manema labarai ranar Asabar a Port Sudan.

Amurka ta buɗe wani shirin tattaunawa a Switzerland ranar 14 ga watan Agusta da zummar kawo ƙarshen bala'in da yaƙi ya jefa ƙasar ta Sudan.

Wakilan RSF sun halarci wurin tattaunawar, sai dai gwamnatin Sudan ba ta amince da tsarinsa ba, kuma ba ta je wurin taron ba, ko da yake ta yi magana ta wayar tarho da masu shiga tsakani.

Saudiyya da Switzerland, da Tarayyar Afirka da Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Majalisar Ɗinkin Duniya na cikin mahalarta taron wanda ke neman samar da dawwamammen zaman lafiya a Sudan.

Sun kammala taron ranar Juma'a ba tare da cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ba ko da yake an samu ci gaba game da shigar da kayan agaji ƙasar ta wasu muhimman hanyoyi.

Yaƙin Sudan ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda kimamin mutum miliyan 25 a faɗin ƙasar suke fama da bala'in yunwa.

AFP