Sojojin kasar Sudan sun ƙaddamar da hare-hare ta sama a babban birnin kasar a jiya Alhamis a wani samame mafi girma na sake samun galaba a can a yakin da suka kwashe watanni 17 suna yi da dakarun Rapid Support Forces (RSF) kamar yadda shaidu da majiyoyin soji suka bayyana.
Yunkurin da sojojin suka yi, wadanda suka rasa iko da galibin babban birnin kasar a farkon rikicin, ya zo ne gabanin jawabin da kwamandansu, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya yi, a taron Majalisar Dinkin Duniya da ke New York a yammacin jiya.
Shaidu sun ba da rahoton tashin bama-bamai da faɗace-faɗace a lokacin da dakarun soji ke ƙoƙarin ƙetara gadojin kogin Nilu da ke hade garuruwa uku da ke maƙwabtaka da su da suka ƙunshi babban birnin kasar, Khartoum, Omdurman da Bahri.
Ko da yake sojojin sun sake ƙwace wani yanki a Omdurman a farkon wannan shekara, sun dogara ne a kan manyan bindigogi da hare-hare ta sama kuma sun kasa kakkabe ingantattun dakarun RSF na kasa da suka jibge a wasu sassan babban birnin kasar.
Har ila yau, kungiyar ta RSF ta ci gaba da samun ci gaba a wasu sassan kasar Sudan a 'yan watannin baya-bayan nan, a rikicin da ya haifar da bala'in jinƙai, wanda ya raba mutane sama da miliyan 10 da muhallansu, tare da jefa sassan kasar cikin matsananciyar yunwa.
Yunkurin diflomasiyya na Amurka da sauran manyan kasashen duniya ya ci tura, inda sojojin suka ƙi halartar tattaunawar a watan da ya gabata a kasar Switzerland.