Rundunar tsaron Nijeriya ta ce dakarun tsaron kasar sun kashe ‘yan ta’adda 191, sun kama 184 sannan sun kubutar da mutum 91 da aka yi garkuwa da su a wasu samame daban-daban da suka ƙaddamar a faɗin ƙasar.
Rundunar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da TRT Afrika ta samu, wacce aka fitar bayan wani taron manema labarai da rundunar ta yi a Abuja a ranar Alhamis, inda ta bayyana wasu nasarori da sojojin suka samu cikin mako guda.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Manjo Janar Edward Buba ta ƙara da cewa mayaƙan Boko Haram 104 da su da iyalansu duk sun miƙa wuya ga sojoji, sannan an kuma kama mutum 22 da kitsa satar ɗanyen man fetur.
“Amma dakarun sun ƙaryata batun an sace ɗanyen fetur na kimanin sama da naira miliyan 388,” sanarwar ta faɗa.
Baya ga haka sojojin Nijeriya a cikin mako gudan sun yi nasarar ƙwace manyan makamai 209 irinsu bindigar AK47 da PKT da bindiga ƙirar gida 11 da ribola 9 da gurneti ta hannu 36 da sauran manyan bindigogi da kuma jigidar harsasai 2,894.
Kazalika an yi nasarar ƙwato motoci 14 da babura tara da keke bakwai da wayoyin hannu 24 da adduna 15 da wasu makaman daban da kuma kudi har sama da naira miliyan 55 duka a hannun ‘yan ta’addar da wasu masu laifukan.
Waɗannan kame da samame da aka yi ya haɗa da arewa da kudancin ƙasar ne, inda ayankin Neja-Delta sojoji suka gano tare da lalata wasu maɓoyun masu laifi 38 da ƙwace kwale-kwale 21 da tankunan da suke ajiyar fetur da durom-durom dasauran wasu kayayaykin da kuma ɗanyen fetur har lita 54,400.
Sannan rundunar tsaron ta ce dakaru ba za su gajiya ba wajen yaƙi da masu tsattsauran ra’ayi, inda ta ce ta bankaɗo wasu ayyuka da suke yi na azurta kansu ta hanyar kashe mutane.
Cikin yankunan da ake yi wannan samame har da jihohin Borno da Yobe masu fama da Boko Haram a arewa maso gabas, sai kuma wasu jihohin arewa maso yamma inda ta yi samamen kan ƴan bindiga da kuma Nej-Delta mai arzikin man fetur da sojoji suka dirar wa ɓarayin ɗanyen fetur.