Sojojin Nijeriya suna fafatawa da mayakan Boko Haram da masu garkuwa da mutane a sassan kasar

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe 'yan bindiga 56 a fadin kasar cikin mako biyun da suka gabata.

A wata sanarwar da ya fitar, darakatan watsa labarai na sojin Nijeriya, ManjorJanar Musa Danmadami, ya ce sojojin sun kuma kama ‘yan bindiga 36 a arewa maso yammacin kasar.

Ya kara da cewar sojojin sun kama masu taimaka wa 'yan Boko Haram takwas tare da ceto fararen hula 119.

Sanarwar ta bayyana cewar mayakan Boko Haram da iyalansu 1,506 sun mika wuya ga sojojin Nijeriya a lokacin.

Ya ce sojojin saman Nijeriya sun yi luguden wuta kan mayakan Boko Haram a wurare daban-daban a jihohin Yobe da Borno inda mayaka da yawa suka mutu.

A cewarsa, sojoji sun kama ‘yan bindiga 28 a arewa maso tsakiyar Nijeriya da ‘yan bangar siyasa da dama a lokacin zaben da aka yi a ranar 18 ga watan Maris a yankin.

TRT Afrika