Rundunar sojojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe wasu ƴan bindiga da suka addabi yankin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna a arewacin ƙasar.
Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai riƙon muƙamin mataimakin mai magana da yawunta, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar ranar Alhamis da maraice.
Laftanar Kanar Yahaya ya ce dakarun nasu sun kuma kuɓutar da mutane da dama da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.
"Dakarun Runduna ta 1 ta Rundunar Sojin Nijeriya da ke sintiri a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ranar 6 ga watan Fabrairun 2024 ta gamu da ƴan bindiga. Yayin da suke gumurzu, dakarun sun kawar da ƴan bindiga huɗu amma wasu sun tsere da raunukan bindiga," in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa ta ƙwato makamai da suka haɗa da bindigogi da alburusai da babura da ƴan bindiga ke amfani da su wurin kai hare-hare.
Haka kuma rundunar ta ce ranar 7 ga watan nan dakarunta sun samu bayanan sirri na ƴan bindiga da suka sace wasu mutane a ƙauyen Kwaga na Birnin Gwari inda suka yi musu dirar mikiya lamarin da ya sa suka tsere.
Dakarun sun kuɓutar da mutum goma sha ɗaya da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su, a cewar Laftanar Kanar Yahaya.
Yankin na Birnin Gwari na cikin wuraren da ƴan bindiga suke yawan kai wa hare-hare inda suke kashe mutane sannan su yi garkuwa da wasu. Sai dai a baya bayan nan rundunar sojin Nijeriya ta ce ta zage dantse wajen magance matsalar.