Nijeriya na amfani da jiragen yaki wajen fatattakan barayin daji:Hoto/Facebook/Nigeria Air Force HQ

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta bayyana cewa dakarunta na Operation Hadarin Daji sun halaka ‘yan ta’adda sama da 80 a Katsina.

Sojojin sun kai samamen a ƙauyen Gidan Kare da ke Ruwan Godiya a Ƙaramar Hukumar Faskari da ke Jihar Katsina, kamar yadda mai magana da yawun sojin sama Edward Gabkwet ya tabbatar.

Ya bayyana cewa baya ga ‘yan ta’addan da sojojin suka kashe, akwai kimanin babura 45 da suka ƙona.

“Samamen ya zama dole bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ‘yan ta’addan sama da 100 suna ta ƙona gidaje a wani ƙauye da ke da nisan kilomita 5 daga Gidan Kare. Da da misalin 8:30 na dare, an ga cewa akwai gidaje da yawa waɗanda ke ci da wuta baya ga ruɗani da aka shiga a ƙauyen,” in ji sanarwar.

“Bayan lokaci kaɗan, sai aka ga babura 12 suna barin ƙauyen inda aka bi sawunsu zuwa wani wuri kusa da ƙauyen Gidan Kare da sansanin Kuka Shidda, inda a nan suka haɗu da sauran ‘yan ta’adda masu yawa.

“Daga nan ne aka ga wasu ‘yan ta’addan suna isowa wanda hakan ya nuna cewa mahaɗa ce ‘yan bindigan ke yi na shirin kai hari ƙauyukan da ke maƙwabtaka,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

“Bayan samun irin wannan damar da ba a cika samunta ba, sai aka nemi umarni kuma aka bayar inda aka kai hari a daidai wurin da misalin 9:40 na dare inda aka kashe ‘yan ta’adda sama da 80 da ƙona babura 45, inda aka ga wasu ‘yan ta’addan da ba su mutu ba suna gudu suna ɗangyashi.”

Jihar Katsina na daga cikin jihohin arewacin Nijeriya da ke fama da matsalar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Ana yawan samun rahotannin ‘yan bindigar na kai hare-hare inda suke satar mutane da kisa da cin zarafin mata.

Ko a makon da ya gabata sai da ‘yan bindigar suka kashe aƙalla mutum 26 a Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara, daga ciki har da ‘yan sanda huɗu.

TRT Afrika