Wannan samame na zuwa ne makonni kadan bayan kashe-kashe da rikicin da aka dinga samu a jihar ta Filato. Hoto: Nig Army

Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta gano wani waje da ake ƙera makamai a Jihar Filato tare da gano tarin makamai da harsasai.

“A ƙoƙarinta na wanzar da zaman lafiya a yankunan Jihar Filato da masu aikata miyagun laifuka ke tada zaune, dakarun rundunar Hakorin Damisa IV a wani samame, sun gano wani waje da aka mayar da shi na ƙera makamai a can wani tsauni a ƙauyen Pakachi na ƙaramar hukumar Mangu,” a cewar sanarwar da rundunar sojin ta fitar ranar Laraba.

Wannan samame na zuwa ne makonni kadan bayan kashe-kashe da rikicin da aka dinga samu a jihar ta Filato, wadanda suka jawo asarar dumbin rayuka da dukiyoyi.

A yayin samamen, an gano makamai masu yawa tare da kama wani mutum ɗaya. “An kama wani mutum mai suna Mr. Tapshak Plangji mai shekara 25 da ake zargin yana da hannu a haramtattun ayyuka a masana’antar,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Ta kuma ce ainihin mamallakin masana’antar mai suna Mr. Nuhu Meshack ya gudu amma ana neman sa don gurfanar da shi a gaban shari’a.

Makaman da rundunar ta gano a masana’antar sun haɗa da bindiga samfurin AK47 tara, da jigidar harsasai 16 da ƙananan bindigogi 11 da zarto uku da gudumomi da injin tono da sauran manyan makamai.

Mr. Plangji da duka makaman da aka samu suna wajen rundunar sojin don yin bincike.

Rundunar ta kuma sha alwashin ci gaba da aiki ba kama hannun yaro don gano duk wasu ɓata gari masu mummunar aniya wajen tarwatsa zaman lafiya a jihar da ma fadin Nijeriya.

TRT Afrika