Rashin tsaro na daga cikin matsalolin da Nijeriya ke fama da su. / Hoto: NA

Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da ceto mutum 78 waɗanda mayaƙan ISWAP suka yi garkuwa da su a Arewa Maso Gabashin Nijeriya.

Rundunar ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar inda ta ce dakarunta na rundunar ta 7 ne suka yi wannan aikin.

Sojojin sun ce daga cikin mutum 78 da suka ceto, an samu mata 35 da yara 43.

“A yayin wani samame mai ƙarfi da aka kai a ranar 22 ga watan Maris ɗin 2024 wanda sojojin yaƙi na rundunar suka kai, sojojin sun yi nasarar fatattakar ƴan ta’adda a ƙauyuka shida da ƴan ta’addan suke riƙe da waɗanda suka yi garkuwa da su.

“A lokacin samamen, sojojin sun yi musayar wuta da su inda har suka kashe yan ta’adda shida. Jajirtattun sojojin kuma sun ceto mutum 78 waɗanda suka haɗa da mata 35 da yara 43 da ƴan ta’ddan suka yi garkuwa da su,” in ji sanarwar.

Ƙauyuka da maɓoyar ƴan ta’adda da sojojin suka kai samame sun haɗa da Ngurusoye da Sabon Gari da Mairamri 1 da Mairamri 2 da Bula Dalo da Bula Dalo extension.

Haka kuma sojojin sun ce sauran wuraren da suka fatattaki ƴan ta’addan sun haɗa da Yamanci da Gargaji.

Daga cikin abubuwan da aka samu daga hannun ƴan ta’addan akwai tuta da wayar salula mallakar wani ɗan ta’adda.

Sanarwar ta kuma ce waɗanda aka ceton na hannun jami’an na soji inda za a yi bincike a kansu.

TRT Afrika