Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta sanar da cewa tana neman mutum 97 ruwa-a-jallo kan zarginsu da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi da kuma barazana ga tsaron Nijeriya.
Manjo Janar Edward Buba wanda shi ne daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a Abuja.
Mutanen da ake nema sun ƙunshi ƴan ta’adda da kwamandojinsu daga Arewa Maso Gabas da Arewa Maso Yamma da Arewa Maso Tsakiya da Kudu Maso Gabashin Nijeriya.
Bisa sunaye da hotuna da hedikwatar tsaron ta fitar, mutum 43 daga Arewa Maso Yammacin Nijeriya suke inda daga cikinsu akwai Alhaji Shingi, Malindi Yakubu, Boka, Dogo Gide, Halilu Sububu, Ado Aliero, Bello Turji, Dan Bokkolo, Labi Yadi, Nagala, Saidu Idris, Kachalla Rugga da Sani Gurgu.
A Arewa Maso Gabashin Nijeriya kuwa wanda yanki ne da Ƙungiyar Boko Haram ta addaba, akwai mutum 33 da hedkwatar ta lissafo waɗanda ta ce su ne suka addabi yankin.
Daga cikinsu akwai Abu Zaida, Modu Sulum, Baba Data, Ahmad, Sani Teacher, Baa Sadiq, Abdul Saad, Kaka Abi, Mohammad Khalifa, Umar Tella, Abu Mutahid, Mallam Mohammad, Mallam Tahiru Baga, Uzaiya da Ali Ngule.
A Arewa Maso Tsakiya da Kudu Maso Gabas mutum 21 ne hukumar ta sanar tana nema.
Daga cikin waɗanda ake nema Kudu Maso Gabashin Nijeriya akwai jagoran ɗayan reshen ƙungiyar IPOB Simon Ekpa.
Haka kuma Chika Edoziem, Egede, Zuma, ThankGod Gentle, Flavour, Mathew, David Ndubuisi, High Chief Williams Agbor, Ebuka Nwaka da kuma Friday Ojimka.