Sojojin Nijar sun yi maraba da shirin Faransa na ficewa daga kasar./Hoto:OTHER

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun bayyana cewa suna so a shirya wani "jadawali" kan ficewar dakarun Faransa daga kasar wadda ke a Yammacin Afirka.

Sabuwar gwamnatin sojin, wadda ta hambarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum watanni biyu da suka gabata, a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata game da janyewar sojojin Faransa daga Nijar ta ce "dole ne a yi jadawali wanda za a tattauna a kansa wanda duka bangarorin za su amince da shi".

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a ranar Lahadi ya sanar da cewa kasarsa za ta janye jakadanta daga Nijar, sannan ta janye sojojinta a watanni masu zuwa.

Ya kara da cewa an kawo karshen kawancen soji da ke tsakanin kasarsa da Nijar don haka dakarun Faransa za su fita daga kasar "nan da makonni da watanni masu zuwa" inda rukunin karshe na sojojin zai bar Nijar a karshen shekarar nan.

Sojojin Nijar sun umarci jakadan Faransa Sylvain Itte ya fita daga kasar bayan da "ya ki amsa gayyatar" ma'aikatar harkokin waje don halartar wani taro da kuma "wasu matakai da Faransa ta dauka da suka ci karo da muradan Nijar".

Awanni 48 da aka ba shi ya fita daga kasar a watan Agusta sun wuce ba tare da ya fita ba, sannan Faransa ta ki amincewa da sojojin da suka yi junyin mulki.

Shugabannin Nijar sun yi maraba da sanarwar Faransa inda suka ce suna jira hukumomin kasar su aiwatar da abin da suka furta a aikace.

Macron ya jaddada matsayin Faransa cewa sojojin "sun yi garkuwa" da Bazoum yana mai cewa a iya saninsu shi ne "halastaccen shugaba Nijar".

TRT Afrika da abokan hulda